2027: INEC ta ƙi karɓar sunan Jonathan a matsayin ɗan takarar PDP da tsgin su Turaki ya gabatar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta yi watsi da miƙa sunan tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Jonathan a gare ta da tsagin jagorancin jam’iyyar PDP na su Kabiru Turaki ya yi ta wani kundi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027, tana mai cewa za a iya yin hakan ne kaɗai ta sahihin shafinta na yanar gizo.

Hakan na zuwa ne bayan da tsagin a ranar Juma’a ya tirje akan ya miƙa wa hukumar suna Jonathan da wasu a matsayin sunayen ‘yan takarar jam’iyyar a zaɓen na 2027 da ke cigaba da ƙaratowa, lamarin da ke ƙara nuna ƙamarin rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar.

Da take tsokaci kan iƙirarin, Daraktar Wayar da kan masu Zaɓe da Hulɗa da Jama’a ta INEC, Victoria Eta-Messi, ta ce hukumar ba ta karɓar sunayen ‘yan takara ta hanyar da ba ta yanar gizo ba.

“Ana miƙawa ne kaɗai ta sahihin sahfinmu bisa biyayya ga sharuɗɗa da dokokinmu,” inji ta.

Saidai Sakataren yaɗa labaran su Turaki, Kwamared Ini Ememobong ya bayyana cewa, kwamitin ya yanke shawarar miƙa jaddawalin sunayen ‘yan takarar nasu ne ta takarda saboda ba a ba su lambobin damar shiga shafin INEC ba a hukumance.

A cewarsa, bayar da lambobin mataki ne na sauƙaƙe lamuran gudanarwa ba buƙatar shari’a ba a dokance acikin kundin dokar zaɓe.

Ya ƙara da cewa, INEC ta amince da jaddawalinsu da ya ƙunshi sunan Jonathan da kuma ‘yan takarar kujerun gwamna, ‘yan majalisun dokokin ƙasa da na jihohi duk da cewa akwai rashin amincewa da tsagin daga ɓangaren hukumar.

By Babaji