
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Abokin tafiyar ɗan takara shugaban ƙasa a zaɓen 2027 na jam’iyyar NDC ya yi kira ga kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ADC da ya mayar da hankali akan abin da ya kira da “muhimman zarge-zarge” akan ɗan takarasa na zaɓen 2027, Alhaji Atiku Abubakar.
Tsohon gwamnan Jihar Kanon ya bayyana haka ne yayin martani ga kalaman kwanan nan na kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC da ke zargin sa da ƙoƙarin kassara ƙarfin ɓangaren adawa da faɗaɗa damarmakin samun nasarar Shugaba Bola Tinubu a 2027.
A wata sanrwa da Daraktan yaɗa labaran kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC (ADC-PCC), Kola Ologbondiyan ya fitar, ya zargi Kwankwaso da caccakar jagororin adawa a madadin sukar gwamnatin APC ta Shugaba Bola Tinubu. Hakan ya biyo bayan kiran da Kwankwaso ya yi wa Atiku na ya janye takara tare da mara wa ɗan takarar NDC, Peter Obi baya a zaɓen na 2027. ADC-PCC ta bayyana wannan kira a matsayin “rashin imani da wakiltar kai”, inda ta yi zargin cewa hakan yunƙuri ne na rarrabar kan ‘yan adawa don amfanin APC.
Saidai, a wata sanrwa da ya fitar a ranar Lahadi, Kwankwaso ya ce, zai fi dacewa ADC-PCC ya karkata ga bai wa ɗan takararsa kariya a madadin caccakar sa ko Obi. “Zai fi kyau a ce ADC-PCC ya bayar da ƙarfinsa wajen musanta manyan zarge-zargen da aka yi akan ɗan takararsa daga ɓangaren Mai Girma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima a madadin kai min hari da Mai Girma Peter Obi,” inji Kwankwaso.
Tsohon gwamnan na Kano ya kuma zargi ADC da yunƙurin nun shi da Obi a idon al’umma a matsayin masu yi wa APC aiki da cewa akwai yiwuwar su janye wa ɗan takara guda ana gab da zaɓen, inda ya ce ba za su taɓa yin hakan ba kuma za su cigaba da kasancewa masu ƙwarin-gwiwar samun nasara.
A cewarsa tikitin takarar Obi da Kwankwaso ya duƙufa ne wajen warware matsalolin rashin tsaro, ilimi, noma, lafiya, ababen more rayuwa da kuma ƙalubalen tattalin arziƙi, yana mai kira ga magoya bayansu da su cigaba da ba su goyon bayan da domin samun nasara a 2027.
