Daga JOHN D WADA a Keffi
Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Kudancin jihar Nasarawa sun bayyana tsohon shugaban NASENI Farfesa Injiniya Mohammed Sani Haruna a matsayin wanda yafi dacewa ya gaji gwamnan jihar mai barin gado wato Injiniya Abdullahi Sule a zaɓen 2027 dake zuwa.
Da yake jawabi a wajen wani babban gangami da masu ruwa da tsakin daga shiyar suka shirya wa Farfesa Injiniya Mohamed Sani Haruna a birnin Lafiya wanda ya haɗa gangamin Alhaji Ibrahim Hamza ya bayyana tabbacinsu cewa Farfesa Injiniya Mohamed Sani Haruna shine mafi dacewa da zai gaji gwamna Abdullahi Sule a 2027 don ɗorawa daga inda gwamnan zai tsaya a ayyukan cigaba a faɗin jihar baki ɗaya.
Alhaji Ibrahim Hamza ya jaddada cewa Farfesa Injiniya Mohamed Sani Haruna ne kaɗai cikin duka ‘yan takaran kujerar gwamnan jihar a yanzu ke da duka ƙwarewa da sanin makaman aiki irin ta gwamna Abdullahi Sule kasancewar dukansu biyun Injiniyoyi ne da suke da wayewa da kuma kusantar al’umma musamman a yankunan karkara da sauran sassan jihar baki ɗaya.
Ya cigaba da bayyana cewa” Kunga idan ku ka lura za ku ga shi Gwamna Abdullahi Sule yayi karatun fasahar sana’ace wato technical school inda ya fara gina tafiyarsa kenan kafin ya kuma shiga fannoni dake zaman kansu wato private sectors inda ya samu ƙwarewa da ake buƙata ba a jihar nan kaɗai ba har da duniya baki ɗaya da hakan yasa a yau ake cigaba da samun waɗannan gagaruman ayyukan cigaba a jihar nan da ƙasa baki ɗaya.
“Sai gashi yau Allah yana shirin kawo mana wani mai kamar sa dake da irin ƙwarewar nasa wato mai girma Farfesa Injiniya Mohamed Sani Haruna. Saboda haka dole ne mu fito ƙwanmu da kwarkwata muyi wannan kira.” Inji shi.
Haka suma a nasu ɓangaren da suke jawabi daban-daban a wajen gagarumin gangamin shugabannin al’umma a matakai daban-daban da sauransu wanda duk suma sun jaddada kyawawan halayyar Farfesa Injiniya Mohamed Sani Haruna inda duk suka kuma tabbatar cewa tabbas shi yafi duka ‘yan takaran kujerar ta gwamna da cewa ya gaji gwamna Abdullahi Sule a 2027, inda suka kuma yi amfani da damar suka shawarci sauran’ ‘yan takaran da al’ummar jihar baki ɗaya su mara masa baya a tafiyar don cimma burin cigaba da gudanar da shugabanci nagari a jihar bayan gwamna Sule ya kammala wa’adinsa
