Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Tsofaffin gwamnonin Jihar Zamfara, Hon. Bello Mohammed Matawalle kuma ƙaramin ministan tsaro da Sanata Abdulaziz Yari sun amince Gwamna Dauda Lawal ya zamo ɗan takarar gwamna a shekarar 2027.
Sun yi wannan jawabin ne a lokacin bikin karɓar gwamnan zuwa jam’iyyar APC wanda mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shatima ya jagoranta a yau Talata da ya gudana a Zamfara Trade fair complex a Gusau.
Matawalle ya buƙaci magoya bayan sa da su goyawa Gwamna Dauda Lawal baya a zaɓen da ke tafe.
“Inaso in sanar da dukkanin magoya bayana cewar daga yau na aminta Gwamna Dauda Lawal shine ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC, kuma ina kira garesu da su goya masa baya a zaɓen dake tafe”. Inji Matawalle
Hakazalika, Sanata Abdulaziz Yari ya bayyana goyon bayansa ga Gwamna Dauda Lawal a matsayin ɗan takarar Gwamna a shekarar 2027.
Sanata Abdulaziz Yari ya ƙara da cewa jam’iyyar APC ta zamo abu ɗaya, yana mai nuni da cewar komawar Gwamna Dauda Lawal Jam’iyyar APC zai kawo haɗin adin kai da cigaban alummar Jihar Zamfara.
Yayi Kira ga mambobin Jam’iyyar APC da magoya bayan sa da su goyawa Gwamna Dauda Lawal baya a zaɓen dake tafe.
