2027: Tinubu da APC sun buƙaci kotu ta yi watsi da ƙarar Atiku ta zargin takardar bogi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar APC da Shugaba Bola Tinubu sun yi kira ga Babbar Kotun Tarayya da ta yi watsi da baki ɗaya ƙorafe-ƙorafen da ƙarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya shigar akan Shugaban Ƙasar ta ƙunsa.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya ruwaito cewa, Atiku ya shigar da Shugaba Tinubu, APC da Hukumar Zaɓeta ƙasa (INEC) ƙara bisa zargin shugaban da gabatar da takardar shaidar kammala hidimar ƙasa ta NYSC ta bogi. Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya nemi kotu ta bayar da izinin soke cancantar Tinubu da jam’iyyar APC daga shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A wata takarda da Tinubu da APC suka shigar a ranar 9 ga Satumba, sun musanta miƙa wa INEC kowace takardar shaida ta bogi a zaɓukan shugaban ƙasa na 2023 da na 2027. Daraktan harkokin shari’a na APC, Mista Sanusi Sama’ila, wanda ya gabatar da ƙorafin, ya ce Tinubu bai taɓa bayar da wata takarda ta Form CF001 ga INEC domin zaɓen 2023 ko 2027 ba, kamar yadda ɓangaren su Atiku ya yi iƙirari.

A cewar Sama’ila, hukumar NYSC ba ta taɓa musanta bai wa Shugaba Tinubu shaidar kammala hidimar ƙasa ba bayan kammala hidimarsa, yana mai cewa babu wata takardar bogi da ɓangaren su APC ya miƙa wa INEC a zaɓuka biyun kamar yadda aka yi iƙirarin.

Ya ƙara da cewa, Atiku ba ɗan APC ba ne kuma bai yi takara a zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa ba da ya yi silar nasarar Tinubu a matsayin ɗan takara ba, yana mai cewa tun a ranar 11 ga Yuli INEC ta tabbatar da Tinubu a matsayin ɗan takarar bayan tantance bayanan da aka gabatar akansa.

By Babaji

Leave a Reply