2027: Yadda Atiku da wasu gwamnonin PDP ke fafutukar zama ’yan takarar shugaban ƙasa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Akwai fargabar cewa burin zama shugaban ƙasa na tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, na iya rura wutar rikici a jam’iyyar PDP tare da kawo cikas ga sulhuntawar da Olagunsoye Oyinlola ke jagoranta.

A ’yan watannin da suka gabata, kawunan ’yan jam’iyyar ya rarrabu zuwa ɓangarori masu biyayya ga Atiku da kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, har sai da Mohammed wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Ana kallon dukkan mutanen biyu a matsayin dalilan da suka tsunduma jam’iyyar cikin rikici tun bayan faɗuwa zaɓe a 2023.

Domin ganin matakin ya tabbata, Mohammed ya haɗa kai da manyan jiga-jigan da ke son korar Shugaban PDP na ƙasa Umar Damagum daga jam’iyyar.

Sai dai kuma gwamnan Jihar Bauchi mai kishin ƙasa, ya bayyana cewa zai iya janyewa daga takarar ne kaɗai idan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya amince ya koma jam’iyyar ya tsaya takara.

Ya bayyana hakan ne watanni biyu da suka gabata a wani taron da wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna Saɓe Africa Initiatiɓe ta shirya a Abuja.

A cewarsa, ’yan Nijeriya ba su ji daɗin mulkin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Sai dai ya yi amanna cewa Jonathan yana da kwarewar da ake buƙata don gyara tattalin arzikin ƙasar kuma zai yi aiki mai kyau idan aka ba shi dama ta biyu don tafiyar da ƙasar.

Sai dai tsohon shugaban ya yi shiru kan rura wutar raɗe-raɗin da ake yi cewa wataƙila ba shi da sha’awar wannan shawara.

Makonni biyu da suka gabata, Mohammed ya yi wani yunƙuri, kuma ya fito fili ya amince da shugabancin muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, jim kaɗan kafin a soke taron majalisar zartarwa ta jami’iyyar ta ƙasa da aka shirya yi.

Shugaban ƙungiyar Gwamnonin PDP ya yi maraba da shugabancin Damagum a wani taron masu ruwa da tsaki da suka kira domin sassauta takun saƙa tsakanin shugabannin jam’iyyar da ke rikici a cikin kwamitin ayyuka na ƙasa.

Gwamnoni biyar ne kawai daga cikin 13 suka halarci taron.

Waɗannan gwamnoni su ne; Gwamna Bala Mohammed; Ademola Adeleke (Osun), Dauda Lawal (Zamfara), Siminalayi Fubara (Ribas) da Caleb Muftwang (Filato).

Hankalin dai ya tashi ne a watan da ya gabata lokacin da wasu jiga-jigan jam’iyyar da ke biyayya ga Wike suka juya wa Atiku baya, maimakon haka suka matsa ƙaimi wajen neman Makinde kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka zanta da manema labarai da ya nemi a sakaya sunansu, sun ce har yanzu ba su yafewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP kan cushe babbar dama tasu ta komawa mulki a 2023, biyo bayan ƙkn amincewar da gwamnonin biyar suka yi na neman ya janye nan take. Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu.

By ukarofi