Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jihar Kaduna ta ɗauki matsayi na ɗaya a matsayin jihar da ta fi kowacce jiha yawan kuɗaɗen shiga a yankin arewa, inda ta samu zunzurutun kuɗi har Naira Biliyan 62.48 a shekarar 2023.
Wannan dai wani gagarumin ƙaruwa ne daga shekarar da ta gabata inda ta samu Naira biliyan 58.
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ce ta fitar da rahoton kwanan nan, inda ya bayyana yadda wasu jihohi ke ƙoƙari wajen samar da kuɗaɗen shiga duk da ƙalubalen tattalin arziki.
A nasa jawabin shugaban hukumar tara kuɗaɗen shiga na jihar Kaduna Jerry Adams, ya ce manufofin gwamnatin Gwamna Uba Sani na hada-hadar kuɗi da faɗaɗa hanyoyin biyan haraji sun haifar da ɗa mai ido wajen ƙaruwar kuɗaɗen shiga a cikin gida a Kaduna.
Da yake lura da cewa, ba abin mamaki ba ne a ce jihar Kaduna ta kasance kan gaba wajen tara kuɗaɗen shiga a shekarar 2023 da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta gudanar, Adams ya ce abin yaba wa Gwamna Uba Sani ne kan yadda ya sarrafa tsarin haraji a Jihar Kaduna da kuma samar da ayyuka cikin tsari.
A cewarsa, KADIRS ce ɗaya tak ke jan ragamar harkokin biyan haraji ta tashar da ake kira “Pay Kaduna Portal,” wanda ke bai wa ‘yan jihar damar biyan haraji daga ko ina, ba tare da zuwa ofisoshin hukumar haraji ba.
“Wannan aikin ya rage walwahalu sosai wajen biyan haraji. Ta hanyar danna gunkin haraji na musamman, mai biyan haraji zai iya biyan harajij sa cikin sauƙi, da sauransu,” inji Adams.
Shugaban zartaswar ya kuma yi nuni da cewa gwamnatin Gwamna Uba Sani ta faɗaɗa hanyoyin biyan haraji ba tare da ƙƙra haraji a jihar Kaduna ba.
Ya ƙara da cewa, KADIRS ta fara faɗaɗa ayyukan haraji cikin sauƙi tun watan Yulin shekarar da ta gabata, saɓanin yadda aka yi a baya wanda ya haifar da koma-baya.
Shugaban Hukumar KADIRS ya kuma bayyana cewa gabaɗaya manufofin Gwamnatin Jihar Kaduna sun taimaka matuƙa wajen inganta yawan haraji da tattalin arzikin jihar.
