Sana’a ce maganin rashin aikin yi a yanzu – Farfesa Sa’adatu Liman ga matasa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Shugabar Babbar Jami’ar Jihar Nasarawa, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta buƙaci matasa a ƙasar nan baki ɗaya su tashi su kama sana’a don magance matsalar rashin aikin yi.Shugabar ta yi kiran ne a wajen wani taro na musamman don bajekolin kayayyakin kere-kere na ɗaliban sashin koyon sana’oi na babbar jami’ar na shekarar 2024 da ake ciki.

Ta ce ba shakka kasancewa ba kowa ba ne zai samu damar aikin gwamnati akwai buƙatar matasa su tashi su kama sana’oi daban-daban su kuma riƙa nuna hazaƙa a yayin koyon nasu don dogara da kai.

Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta kuma yi amfani da damar inda ta yi kira na musamman ga shugabanni ‘yan siyasa a ƙasa baki ɗaya su tallafa tare da ƙirƙiro da hukumomin koyon sana’o’i na zamani da shirye-shirye na musamman a fannin don ƙarfafa wa matasan gwiwa don suma su iya bada gudumawansu ga cigaban ƙasa.

Har ila yau shugabar jami’ar ta gwamnatin jihar Nasarawa Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta kuma yaba wa malamai da ma’aikatan sashin koyon sana’o’in na jami’ar dangane da ƙoƙari da suke yi wajen renon ɗaliban ta ɓangaren sana’o’in inda ta nanata buƙatar ɗaliban su rungumi sana’ar da gaske.

A nata ɓangaren ita ma da take jawabi shugabar sashin na koyon sana’o’i na jami’ar Dakta Monica Agu ta bayyana cewa an kafa cibiyar ne da nufin bai wa ɗaliban jami’ar damar samun ilimin sana’o’i daban-daban musamman na zamani don agaza wa kawunansu da cigaban ƙasa baki ɗaya.

Sauran shugabanni a duka matakai da suka halarci taron suka kuma yi jawabi duk sun yaba wa hangen nesa na Farfesa Sa’datu Hassan Liman dangane da cigaba da tallafa wa shashin don bunƙasar shirin na koyon sana’o’in a jami’ar da jihar dama ƙasa baki ɗaya da take cigaba da yi kawo yanzu kana suma suka shawarci ɗaliban kada su yi wasa da damar.

Sauran abubuwan da aka gudanar a yayin taron sun haɗa da baje kolin kayayyakin ƙirar hannu da ɗaliban suka ƙera da kansu da dai sauransu.

By ukarofi