2027: ‘Yan adawa sun sanya ranar sake zama don ƙulla yarjejeniyar tsayar da ɗan takara guda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Haɗakar jam’iyyun adawa da ke naman ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyya mai mulki APC za zaɓen 2027, ta ayyana ranar 30 ga Nuwamba a matsayin lokacin da za ta yi zama don ƙulla yarjejeniyar sabunta dimukraɗiyya. An ɗage zaman ne da mako guda yayin da ake ƙoƙarin tattara kan jagororin jam’iyyu da ‘yan takarar shugaban ƙasa da ke cikin haɗakar.

Tsohon Darakta-Janar na ƙungiyar gwamnoni ta Progressives Governors Forum, Salihu Lukman ne ya sanar da haka a wata hira da gidan talabijin na Arise, inda ya ce an ɗage taron ne biyo bayan shawarwari da jagororin jam’iyya da ‘yan takarar shugaban ƙasa.

A cewarsa, haɗakar ta buƙaci shugabannin jam’iyyu, ‘yan takarar shugaban ƙasa da abokan tafiyarsu su halarci taron wanda za a gudanar a Abuja, inda ake sa ran cimma matsaya guda.

Ya ce, yayin da wasu suka ce sun shirya halarta, wasu kuwa cewa suka yi a ba su ƙarin lokaci domin samun damar aiwatar da wasu gyare-gyare kan tarukan yaƙin neman zaɓensu. Don haka ne haɗakar ta amince da ɗage zaman zuwa ranar 30 ga Nuwamba daga ranar da aka sanya da fari.

Haɗakar ta ƙunshi jam’iyyu shida da suka haɗa da tsagi-tsagi, ciki har da African Democratic Congress, Allied Peoples Movement, National Democratic Congress, tsagin Peoples Democratic Party na su Tanimu Turaki, People’s Redemption Party da kuma Social Democratic Party. Hakan na da nufin ƙulla yarjejeniyar siyasa gabanin zaɓukan 2027.

By Babaji

Leave a Reply