Gwmanatin Kano ta ayyana 25 ga Yuli a matsayin ranar fara hutun ɗaliban firamare

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da Juma’a, 25 ga watan Yuli, 2025 a matsayin ranar fara hutun ƙarshen zango na uku ga ɗaliban makarantun firamare da na ƙasa da su a jihar.

Don haka ta shawarci iyaye da wakilan ɗaliban makarantun kwana su shirya ɗauko ƴaƴansu a safiyar ranar.

A wata sanarwa da Daraktan wayar da kan al’umma na Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Ƙiru ya fitar, gwamnatin ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana da za su koma ne a ranar Lahadi, 7 ga watan Satumba, yayin da na je-ka-dawo kuma za su koma a washe-garin ranar.

Ya ce, kwamishinan ma’aikatar, Dakta Ali Haruna Makoɗa ya yi kira ga iyayen ɗalibai da su tabbatar da bada haɗin kai game da ranakun koma wa makarantun.

Haka kuma ya yi gargaɗin cewa za a hukunta ɗaliban da suka ƙi kiyaye lokacin komawar.

Kazalika, yi godiya ga iyaye da ɗaukacin al’ummar jihar bisa ba su haɗin kai wajen tafiyar da harkokin ma’aikatar yadda suka dace a faɗin jihar.

By Babaji