
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba Majalisar Dattawa ta marabci sanatoci guda huɗu da suka sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC, lamarin da ya yi sanadin ƙara wa jam’iyyar mai mulki ƙarfi a majalisar.
Sanatocin sune Ekong Samson (Akwa-Ibom ta Kudu), Etim Bassey (Akwa-Ibom Arewa maso Gabas), Francis Fadahunsi (Osun ta Gabas) da kuma Olubiyi Fadeyi (Osun ta Tsakiya).
A yayin karɓar sababbin mambobin majalisar ta sassauta dokokinta, inda ta bar wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar suka halarci zaman waɗanda suka haɗa da Sakataren APC, Ajibola Basiru; Shugaban APC a Osun Tajudeen Lawal; mambobin majalisar wakilai da kuma tsohon minista, Chris Ngige.
Da sabon ci-gaban ne APC ta ƙara mamaye kujerun majalisar inda a yanzu ta ke da 72 daga guda 50 da ta ke da su a shekarar 2023.
Haka kuma, lamarin ya sa adadin kujerun da PDP ke da su ya koma 26 da ma wasu ƴan jam’iyyun LP da NNPP.
Shugaban mafiya rinjaye a majalisar, Opeyemi Bamidele ya bayyana hakan a matsayin yunƙurin na ƙarfafa tafiyar da harkokin dimukraɗiyya wajen ciyar da Nijeriya gaba.
