
Mataimakin Kwamandan Hisba, mai Kula da Shiyyar Bichi, ACG Malam Abubakar Isa ya jinjina wa shugabancin ƙungiyar ƴan kasuwa ta ‘Traders Multi-Purpose Cooperative Society, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abubakar Muzahim Saleh bisa rawar da suka taka wajen hana baɗala, caca a lunguna da saƙo-saƙo na kasuwar, a yayin wata ziyara da suka kai masa a ofishinsa.
Ya kuma ja hankalinsu cewa kasuwar ta Bichi zaɓi ne daga Allah, don haka su tafiyar da ni’mar da Allah ya ba su ta hanyar tsoronsa.
A ɓangarensa, Kwamandan Hisba, Malam Murtala Sufyanu ya ƙara musu da nasihar rike gaskiya da amana da gujewa tauye mudu da algus da almundahana, gami da alkawarin aiki tare da su domin inganta kyawawan dabi’u na addini da kuma al’ada acikin kasuwancinsu.
Sannan ya buƙaci shugaban kasuwar ya samar musu ofis da za su ajiye jami’ansu domin ci gaba da dakile ayyukan barna na batagari a cikin kasuwar.
A Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), mai Kula da Shiyyar Bichi, Alhaji Abdullahi Chiranci, ya ce, wannan ziyara ita ce ta farko da ya karba daga ‘yan kasuwa tun kama aikinsa a Karamar Hukumar Bichi, shi ma ya yi alkawarin aiki tare da su domin kawar da sha da fataucin miyagun kwayoyi a karamar hukumar.
Ya nemi taimakon mota da babura bisa amfanin jami’an hukumar domin samun nasarar ci gaba da ayyukansu yadda yakamata.
A wani ɓangare na ziyarar, a Hukumar Tsaro ta Civil Defense ta Bichi, Mataimakin Kwamandan Hukumar mai Kula da Shiyyar Bichi, AU Muhammad ne ya tarbi ‘yan kungiyar a ofishinsa, ya kuma nuna jin dadinsa na wannan muhimmiyar ziyara ta cigaba, inda ya jaddada musu cewa hukumarsu ita ce mai kare kadarorin gwamnati tare da yin sulhu a fannin cinikayya.
Sannan ya yi fatan alheri da addu’ar samun ci-gaba mai ɗorewa a kasuwar ta Bichi, kamar yadda jami’ar yaɗa labarai ta Ƙaramar Hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo tabayyana.



