
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Asusun ba da lamunin karatu na ƙasa (NELFUND), ya ce ya raba sama da Naira Biliyan 116.4 ga ɗalibai fiye da 624,000 tun bayan kaddamar da shirin lamunin karatu a ranar 24 ga Mayu, 2024.
A cewar rahoton da ya fitar ta shafinsa na X a ranar Talata, NELFUND ya karɓi sama da rajistar ɗalibai 929,000, inda sama da 624,000 daga cikinsu suka amfana da shirin.
Rahoton ya nuna cewa an amince da sabbin masu rajista su guda 12,398, adadin da ya kai ƙarin kaso 1.4 cikin 100 idan aka kwatanta da rahoton da aka fitar a baya.
NELFUND ya bayyana cewa daga cikin kudaden da aka rarraba, an biya biliyan N65.3 kai-tsaye ga makarantu 239 a fadin ƙasar a matsayin kuɗin makaranta, yayin da aka bada N51.1bn ga ɗaliban a matsayin kudin walwala da abinci, inda jimillar kuɗin ta zama biliyan N116.4 zuwa yanzu.
A wani bangare na sanarwar, NELFUND ya ce ya buɗe sabon shafin neman lamunin karatu domin zangon karatu na 2025/2026, wanda zai yi aiki daga Alhamis, 23 ga Oktoba, zuwa Asabar, 31 ga Janairu, 2026.
A cewar darektan sadarwa na hukumar, Oseyemi Oluwatuyi, sabbin masu neman lamuni za su iya amfani da lambar shiga jami’a (admission number) ko lambar JAMB wajen cikawa, maimakon lambar dalibi (matric number).
Hukumar NELFUND dai an kafa ta ne bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar kafa shirin lamunin dalibai a watan Afrilu 2024. Shirin yana bai wa daliban da ke karatu a makarantu na gwamnati damar samun lamuni ba tare da ruwa ba, domin biyan kudin makaranta da kuma samun kuɗin abinci yayin karatu.
Manufar shirin ita ce rage cikas na kudi da ke hana matasa shiga manyan makarantu da kuma bunkasa damar ilimi ga ‘ya’yan talakawa.
Ana sa ran daliban da suka ci gajiyar shirin za su fara biyan lamunin bayan sun sami aikin yi da zarar sun kammala karatunsu.
