Sheikh Yakubu Musa Hassan ya zama ɗan majalisar sarakuna a Katsina

Spread the love

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Radda ya naɗa Shugaban ƙungiyar Izalah ta Jihar Katsina Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan (Sautus-Sunnah) a matsayin ɗan majalisar sarakunan jihar Katsina mai wakiltar malamai.

Takardar naɗin wanda ke ɗauke da sa Aminu Tukur babban sakatare a ofishin sakataren gwamnatin jihar ya ce wannan naɗin na bisa tanadin sashi na 21(1) na dokar sarakunan jihar Katsina.

Haka kuma gwamnan ya amince da naɗin shugaban kamfanin continental Alhaji Salisu Mamman a matsayin ɗan majalisar masarautar Katsina da zai wakilci ƴan kasuwa.

Harwala yau gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da naɗin Alhaji Muhammad Usman Sarki a matsayin ɗan majalisar masarautar Katsina da zai wakilci matasa,sai Alhaji sada Salisu Ruma,Ɗanwairen Katsina a matsayin mataimakin sakatare a majalisar masarautar Katsina.

Duka waɗanda a ka naɗa za su fara aiki nan take kamar yadda takardar sanar wa ya ƙunsa.

By ukarofi