Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Matar Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta ɗauki nauyin mata 200 don yi masu aiki da basu magunguna kyauta masu ɗauke da cutar kansar mahaifa da ta mama a Jihar.
Hajiya Huriyya ta bayyana hakan ne a wani taron wayar da kan jama’a kan ranar cutar kansa ta duniya ta 2025, wanda aka gudanar a makarantar sakandare ta ‘yan mata ta gwamnati a Gusau yau Alhamis.
A cewarta, za a tantance mata 200 a ƙarƙashin ofishinta domin a yi musu magani kyauta da ke ɗauke da cutar kansar nahaifa da ta mama.
Hajiya Huriyya ta ce, taken ranar kamuwa da cutar kansa ta duniya ta wannan shekarar shine “Kowane labari na musamman ne, kowace tafiya tana da muhimmanci”.
“Wannan rana tana tunatar da mu cewa kowane mutum na musamman ne kuma ya cancanci kulawa da tausayi”. Ta ce
“Wannan yana koya mana cewa duk da bambance-bambancenmu, muna da ƙarfi idan muka tsaya cikin haɗin kai da goyon baya”. Ta ƙara da cewa.
Matar Gwamnan ta roƙi mata da su ba da fifiko ga lafiyarsu kuma su ƙarfafa wasu su yi haka.
A cewarta samun ilimi da wayar da kan jama’a game da cutar kansar nono yana da matuƙar muhimmanci a ga ya’ya mata a matsayin su na ɗalibai.
“Zai taimaka muku yin zaɓi mai kyau, kula da lafiyarku da ta wasu da kuma gina makoma mai kyau ga al’ummarmu”.
Huriyya Dauda Lawal ta yaba wa ƙungiyar matan gwamnoni masu yaƙi da cutar Cancer (FLAC) saboda jajircewarsu ga ilmantar da al’ummomi da kuma tabbatar da cewa kowace mace ta sami labarin cutar kansa.
“Jajircewarsu ga wayar da kan jama’a abin yabawa ne ƙwarai da gaske”.
Hajiya Huriyya wacce ita ce sakatariyar ƙasa ta ƙungiyar matan gwamnoni masu yaƙi da Cutar Cancer ta tabbatar wa mata a jihar cewa ofishinta zai ci gaba da wayar da kan jama’a game da cutar kansa, da kuma ƙarfafa gano cutar da wuri, duba lafiya akai-akai a tsakanin mata.
“Za mu ci gaba da aiki ba tare da gajiyawa ba don tabbatar da cewa kowanne ɗan ƙasa yana da damar samun bayanai da suka dace don kula da lafiyarsu”. Ta ce.
Ta yaba wa ƙoƙarin mijinta saboda hangen nesansa na jagoranci wajen fifita harkokin kiwon lafiya da Kuma kawo sauyi mai inganci a fannin kula da lafiya alummar jihar.
“Mijina ya nuna cewa mata, yara da dukkan ‘yan ƙasa suna da damar samun ingantaccen kulawar lafiya cikin sauƙi, wannan kuma ya nuna jajircewarsa ga lafiyar al’ummarmu.” Ta ƙara da cewa.
