An cafke wani mutum da ke bayyana kan sa a matsayin ɗan Majalisar Tarayya na Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Jami’an tsaron farin kaya na humkuma NSCDC sun kama wani mutum wanda aka sakaya sunansa, ana zargin shi da yin sojan gona a matsayin ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta tsakiya a majalisar tarayya.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron sun kama mutumin ne, bayan an same shi da katin shaidar bogi da wasu takardu da ke nuna cewa shi ne ɗan majalisar tarayya.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya yi ƙoƙarin ganin shugaban hukumar tsaron farin kaya ne lokacin da jami’an suka gano cewa takardun nasa na bogi ne.

Binciken jami’an tsaro ya kuma gano cewa sojan gonar ya taɓa samun ganawa da wasu jakadun ƙasashen waje, inda ya yi amfani da wannan matsayin na ɗan majalisar bogi wajen neman amincewarsu.

A cewar majiyarmu, wanda aka kama ya bayyana wa jami’an tsaron cewa ya ɗauki hayar mota ne tare da haɗin kai da wasu mutane da ke taimaka masa wajen aiwatar da wannan ɗanyen aiki.

Binciken da majiyarmu ta gudanar ya gano cewa halastaccen ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, Hon. Sani Aliyu Ɗanlami, ya je ofishin jami’an farin kaya domin sasanta batun, inda ya karɓi wanda ake zargin beli, kuma ya buƙaci a dakatar da shigar da ƙara a kotu.

A yayin hira da jaridar Katsina Times, wanda aka kama ya amsa laifinsa, yana mai cewa ya aikata hakan ne kawai don neman damar samar wa da matasan Katsina ayyukan yi.

Ya ƙara da cewa, “ƙaddara ce ta kawo haka, ina roƙon Allah ya gafarta mini, kuma na yi alƙawarin ba zan sake aikata irin wannan abu ba.”

Mutumin ya kuma gode wa Hon. Sani Aliyu Ɗanlami bisa taimakon da ya yi masa wajen kuɓutar da shi daga tsauraran matakan doka.

By ukarofi