An tasa ƙeyar lauya da wasu huɗu zuwa kurkuku kan ɓatanci ga sanatan Bauchi a TikTok

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta umarci a tsare lauya Ahmed Abdulrahman da wasu mutane huɗu a hannun ƴan sanda bisa zargin su da hannu a ayyukan sharri da tatsar kuɗaɗe daga wajen wani sanata.

Rahotanni sun bayyana cewa Mai shari’ar Rita Ofili-Ajumogobia ne ta bada umarnin a ranar Alhamis bayan gurfanar da mutanen bisa tuhumar su da aikata laifuka 11 da Sufeto Janar na ƴan sanda ya shigar akansu.

Mutanen sune: Daure David, Ishaq Abubakar Muhammed, Abdulrashid Abdullahi Musa, da Nasiru Usman Abubakar.

A cewar bayanan masu shari’ar, ana zargin mutane biyar ɗin ne da ɓata wa Sanata Shehu Buba Umar suna ta ƙafar sada zumunta.

An zarge su ne da wallafa saƙon cin fuska ga Sanatan, wanda shi ne shugaban kwamitin tsaron ƙasa da leƙen asiri da kuma neman tatsar kuɗaɗe daga gare shi.

Saidai, baki ɗaya mutanen sun musanta abinda ake tuhumar sun a kai, lamarin da ya sa cikin hanzari lauyan da ke kare ɓangaren masu shigar da ƙara, Victor Okoye ya nemi kotun da ta bayar da dama na a ajiye su a gidan yarin Kuje har zuwa lokacin da za a cigaba da shari’a.

Haka kuma, lauyoyin ɓangaren waɗanda ake tuhuma ƙarƙashin jagorancin Afeez Matanmi, sun nemi kotu da ta bada belin Abdulrahman a matsayinsa na masanin harkar shari’a, amma hakan bai samu ba.

Daga nan ne alƙalin ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba domin cigaba da shari’ar.

By Babaji