Rikicin Filato: Lalong ya kafa dokar hana fita a wasu sassan jihar

Spread the love

Gwamnatin jihar Filato ta sanya dokar hana zirga-zirga a yankunan ƙananan hukumomin Bassa da Jos ta Arewa da kuma Jos ta Kudu.

Gwamantin Filato ta ɗauki wannan mataki ne biyo bayan hatsaniyar da aka samu a yankin ƙaramar hukumar Jos ta Arewa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da ashirin tare da jikkata wasu da dama.

Cikin sanarwar da ta fito ta hannun Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar a yau Lahadi, Dr Makut Macham, Gwamnan Jihar, Simon Lalong ya ce, dokar hana zirga-zirgar ta soma aiki ne daga ranar 14 ga Agusta, daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Ta bakin Gwamnan, “Na ba da umarnin kafa dokar hana zirga-zirga daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a yankunan ƙananan hukumomin Jos ta Arewa da Bassa da kuma Jos ta Kudu, wadda ta soma aiki daga 14 ga Agusta, 2021.

“Wannan doka za ta ci gaba da aiki har zuwa lokacin da Majalisar Tsaron Jihar za ta ba da bayani.”

Lalong ya yi gargaɗi jama’ar yankunan da lamarin ya shafa da su bi wannan dokar sau da ƙafa, yana mai cewa jami’an tsaro za su ci gaba da sanya ido a yankunan.

Haka nan, ya ce gwamnati sa za ta ci gaba da sanya ido tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen kare rayuka da kuma dukiyoyin ‘yan jihar.

Daga nan, Lalong ya yi kira ga ‘yan jihar da su guji duk wani lamari da ka iya tada zaune tsaye a jihar. Yana mai cewa, jami’an tsaro sun soma gudanar da abincike kan rikicin inda kawo yanzu aka damƙe mutum 20 da ake zargi suna da alaƙa da rikicin.

A ƙarshe, Lalong ya jajanta wa ‘yan’uwan duka waɗanda suka mutu da ma waɗanda suka jikkata sakamakon rikicin.

By Editor