APC ɓangaren Ganduje za su biya tsagin Shekarau tarar Naira miliyan ɗaya, inji kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Abuja da APC tsagin Ganduje suka ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci, inda ta sake jaddada zaɓen da ɓangaren tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau suka ya yi a matsayin halastaccen zaɓe, sannan kuma ta kori ƙarar.

Manhaja ta kalato yadda Alƙalin kotun, Mai Sharia Hamza Mu’azu ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, inda kuma ya umurci ɓangaren Ganduje su biya ɓangaren Shekarau tarar Naira miliyan ɗaya na ɓata masu lokaci.

Kotun ta ƙara jaddada cewa zaɓen APC da ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau suka gudanar na ƙananan hukumomi da kuma mazaɓu da gundumomi ya halasta, kuma su ke da damar zaɓen shugabannin jam’iyya a matakin jiha, inda daga ƙarshe ta kori ƙarar da su Ganduje suka shigar a gabanta.