Daga IBRAHIM YAYA
A yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar COVID-19, a hannu guda kuma hukumomi da masana a fannin yaƙi da sauyin yanayi, na yin gargaɗi game da yadda yunwa da fari za su iya addabar sassan duniya. “Wai ana kukan gargaɗe sai ga karaya”.
Sanin kowa ne cewa, masana sun sha yin kashedi tun kafin ɓullar annobar cutar COVID-19 ta zama wani batu na daban cewa, za a fuskanci mummunan matsalar jin kai da ba a taɓa gani irinta ba, tun a lokacin yaƙin duniya na biyu, saboda wasu dalilai.
Na baya-bayan shi ne, kiran da sama da hukumomin agaji 50 suka yi na gaggauta samar da ƙarin kuɗaɗe da shugabanci na gari don tinkarar gagarumar matsalar ayyukan jin kai dake fuskantar miliyoyin mutanen dake zaune a shiyyar gabashin Afrika sanadiyyar matsanancin fari, har ma aka yi kashedin cewa, muddin aka yi jinkiri, babu makawa rayukan jama’a da dama na iya salwanta.
Ƙungiyar agaji ta Save the Children, da Norwegian Refugee Council, da gamayyar ƙungiyoyi masu zaman kansu a Somaliya, na daga cikin waɗanda suka bayar da wannan gargadi, gabanin taron ƙungiyoyin bada tallafi na ƙasa da ƙasa da za a gudanar a Geneva. Tuni ma alkaluma suka nuna cewa, sama da mutane miliyan 14 a ƙasashen Somaliya, da Habasha da Kenya, kuma kusan rabin adadin ƙananan yara ne, sun riga sun tsunduma cikin mummunan yunwa.
Matsalolin tashe-tashen hankula, da rashin tsaro, da karayar tattalin arziki, suna daga cikin dalilan dake ƙara ta’azzara wannan matsala na tsawon shekaru. Yanzu kuma ga batun matsalar sauyin yanayi, da yadda tarin jama’a ke kauracewa muhallansu, lamarin dake sanadiyyar fadawar ƙarin mutane cikin yanayin tsananin buƙata.
Ganin irin mummunan halin da aka shiga, ya sa masu fashin baƙi ke cewa, yanzu ne lokacin da ya dace na ɗaukar matakai, domin kaucewa fadawar miliyoyin al’ummomin dake shiyyar gabashin Afrika cikin fitina. Tun kafin wankin hula ya kai dare.
