Bikin Sallah: Rundunar ’yan sanda ta baza jami’ai 6,000 a Borno

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta baza jami’ai 6,000 domin samar da tsaro a yayin gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana kamar yadda aka tsara.

Tushen ya biyo bayan barazanar da ’yan ta’adda suka yi na kai hari a ƙananan hukumomin Maiduguri Metropolitan Council (MMC), Bama da Konduga na jihar.

Da ya ke sanar da tura rundunar a ranar Alhamis a Maiduguri, mataimakin Sufeton ’yan sanda (ASP), Sani Shatambay ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun yi barazanar tayar da bomabomai a lokacin bukukuwan Sallah.

“Muna shirye don samar da isasshen tsaro ga rayuka da dukiyoyin mutane kafin, lokacin da kuma bayan bikin Eid-El-Fitr mai zuwa,” inji shi.

Don haka ya bada tabbacin tura jami’an ’yan sanda zuwa harabar quraren sallar idi da sauran wuraren taruwar jama’a a faɗin jihar.

Ya ce, an yi hakan ne domin tabbatar da tsaron lafiyar mazauna wurin a yayin bikin da kuma bayansa.

Ya kuma yi gargaɗin cewa, ’yan sanda ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen daƙile duk wani ɓata-gari da ke son yin amfani da lokacin wajen tada fitina ko kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma.

Ya kuma buƙaci jama’a da su kasance masu lura da tsaro ta hanyar kai rahoton duk wani motsin mutane ga ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro.

By Editor