Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja
Hedikwatar jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta faɗa cikin ruɗani a ranar Larabar da ta gabata yayin da wasu maƙudan kuɗaɗe har Naira miliyan 43 suka ɓace a harabar ofishin.
Kuɗaɗen da ke cikin dala sun kai dalar Amurka 75,000 kuma ana tsammanin suna cikin kuɗaɗen da jam’iyyar ta tara a cigaba da sayar da fom ɗin zaɓen 2023.
Rahotanni sun bayyana cewa, kwatsam aka tayar da rumfar da ake sayar da fom ɗin ba tare da wani bayani ba bayan an gano kuɗin sun vata.
An tattaro cewa, kuɗaɗen da suka kai dala 75,000 sun ɓace a daidai lokacin da ake gwabzawar cunkoson jama’a a babbar ƙofar shiga harabar jam’iyyar.
Sai dai wasu majiyoyin jam’iyyar sun bayyana cewa, kuɗaɗen da suka vata ba su da alaqa da kuɗaɗen sayar da fom ɗin takara, domin ana sa ran masu neman tsayawa takara su yi ajiya a lambobin da aka keɓewa kafin su karɓi fom ɗinsu a gidan Buhari.
“Lokacin da adadin kuɗin suka ɓata, sai aka nemi ɓarawon aka rasa a cikin fili. A lokacin da aka sanar da jami’an tsaro ɓarawon ya ɓace da ambulan,” inji majiyar jam’iyyar.
Da sanyin safiyar ranar Laraba, Sakatariyar ta kasance cibiyar ayyukan ƙudan zuma yayin da masu neman tsayawa takara suka yi tururuwar karɓar fom na ofisoshin zaɓe daban-daban.
Rahotanni sun bayyana cewa, ana cigaba da tattaunawa da shugabannin jam’iyyar APC na mayar da fom ɗin sayar da fom zuwa wani wuri na daban inda za a samu isassun fili da zai ɗauki masu neman takara da magoya bayansu.
Wani muhimmin abin da ya sa ake neman a koma matsugunin shi ne tsaro domin yadda lamarin sace-sacen da aka yi a ranar Laraba ya nuna yadda tsaron hedikwatar jam’iyyar APC ka iya taɓarɓarewa.
