Daga CMG HAUSA
Firaministan ƙasar Sin Li Keqiang, ya jaddada buƙatar aiwatar da manufofin ƙasa, na daidaita ci gaban tattalin arziki, da tallafawa sassan kasuwanni, da bunƙasa samar da ayyukan yi, da inganta rayuwar alumma.
Li, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin ƙolin JKS, ya yi wannan tsokaci ne a jiya Laraba, yayin taron majalissar gudanarwar ƙasar Sin da ya gudana ta kafar bidiyo. Yana mai jan hankali da a ƙara azama wajen ingiza harkokin tattalin arziki bakin gwargwado.
Firaministan ya ƙara da cewa, ana aiwatar da matakai daban daban domin shawo kan wahalhalu, da ƙalubaloli da suka biyo bayan wasu alamura da suka auku a bana.
Ya ce an fuskanci wahalhalu a watan Maris da ma watan Afirilu, waɗanda kusan ta wasu fannonin sun dara na shekarar 2020, lokacin da annobar COVID-19 ta fara ɓulla a ƙasar, lamarin da ya haifar da koma baya a fannonin samar da guraben ayyukan yi, da sarrafa kayayyaki a masanaantu, da sashen amfani da makamashi, da safarar manyan hajoji ta ruwa, da dai sauran su.
Sai dai duk da haka, firaminista Li ya jaddada muhimmancin aiwatar da matakan ingiza ci gaba, wanda ya ce shi ne jigon warware duk wasu matsalolin ƙasar Sin, yana mai kira da tun daga yanzu, a gaggauta aiwatar da matakan dawo da tattalin arzikin ƙasar kan turba ta gari.
Ya kuma umarci da a aiwatar da cikakkun matakai, na ingiza salon ci gaban ƙasar Sin, a kuma tsara matakan shawo kan annobar COVID-19, haɗe da dabarun bunƙasa tattalin arziki da zamantakewar alumma bisa inganci, kana a daidaita ci gaba bisa kyakkyawan matsayi.
Mai Fassarawa: Saminu Alhassan
