Ƙasashe mambobin BRICS sun ƙaddamar da kwamitin haɗin gwiwa game da binciken samaniya

Daga CMG HAUSA

A jiya Laraba ne ƙasashe 5 mambobin ƙungiyar BRICS, suka ƙaddamar da wani sabon kwamitin haɗin gwiwa, wanda zai bude sabon babi ga ayyukan su na amfani da taurarin ɗan adam, da musayar bayanai game da sararin samaniya tsakanin su.

Da yake tsokaci game da hakan ta kafar bidiyo, shugaban hukumar lura da ayyukan binciken sararin samaniya na ƙasar Sin Zhang Kejian, ya ce kwamitin zai tsara ayyukan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen na BRICS, ta yadda za su ci gajiya daga managartan hidimomin sanya ido ta amfani da taurarin ɗan adam, matakin da zai taimaka wajen raya tattalin arziki da zamantakewar su.

Zhang ya ƙara da cewa, sabon kwamitin zai bai wa hukumomin binciken sararin samaniya na ƙasashe mambobin BRICS damar aiki kafaɗa da kafaɗa a fannonin kare muhalli da kandagarkin bala’u daga indallahi, da shawo kan ƙalubalen sauyin yanayi, ta amfani da managarcin tsarin musayar bayanai.

Mai fassara: Saminu