Abinda na fuskanta a jinyar ƙoda na mayar littafi – Sodikat A’isha Umar

“Kallon mahaukaciya aka yi min lokacin da na ce zan fara rubutu”

Daga ABUBAKAR M. TAHEER 

Mai karatu a yau shafinmu na Adabi a jaridarku ta Blueprint Mahaja ya samu baƙuncin matashiyar marubuciya kuma ’yar jarida, wacce jinya ta saka ta zama marubuciyar littafi. Wakilinmu, Abubakar M Taheer, ya samu tattaunawa da ita. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Za ki gabatar mana da kanki ga masu karatunmu.
SODIKAT: Sunana Sodikat Aisha Umar Maimalari. An haife ni a Jihar Legas a shekarar 2001, ranar 6 ga watan Yuni. Na yi firamare na har izuwa matakin sakandirin aji na biyu a Legas, kafin Allah ya yi wa mahaifina rasuwa muka dawo Jihar jigawa, Ƙaramar Hukumar Mallam madori a shekarar 2016. A inda na kammala Secondary school ɗina a May Excellence international school a shekarar 2017, daganan kuma na koma Jihar Kano da zama, na tafi makaranta a Ƙaramar Hukumar Kazaure dake Jihar Jigawa, inda na yi karatu a Jigawa State institute of Information and Technology wato informatics a matakin Advance International diploma a jigawa state institute, na kuma yi certificate na training da dama a fanin Information and Technology. A shekarar 2019, ina kammala makaranta na koma Jihar jigawa na samu aiki a gidan rediyo sawaba dake Hadejiya Jihar jigawa a matsayin reporter kafin daga bisani na zama Sound editor, a haka har na zaman assistant kuma na zaman Head of Studio production. Sannan ni marubuciyar littafi ce, a inda na rubuta littattafai da daman. Domin ko a waccan shekarar da ta gabata nayi ‘launching’ ɗin wani littafina mai taken ‘Cuta Ba Mutuwa Ba’, Wanda yake magana a kan cutar ƙoda wato Acute kidney injury wato AKI wanda infection ke janyowa, wanda ni guda ce daga cikin waɗanda sukanyi fama da wannan cutar kuma na warke.

Littafai nawa kika rubuta?
Da farko na ‘Burin Kowanne Ɗan Adam’ wanda shine littafina na farko da na taɓa rubutawa a shekarar 2020 da yake magana akan burin ɗan Adam wanda ba a taɓa rabashi da buri, sai har ya koma ga mahaliccinsa. sai kuma, ‘Komai Na Da Lokaci’ wanda ke magana akan ‘Drug trafficking’, sai ‘Ina Muka dosa’ inda littafin ke magana a kan yadda za a magance matsalar tsaro a ƙasarnan da sauransu. Bayan rubutu, ina koyarwa a Computer training school ta info village dake cikin garin Hadejia, sannan na koma karatu inda a yanzu haka ina level 300 a National open University wato Noun, sannan ina ɗan taɓa kasuwanci jifa-jifa.
 
Waɗanne ƙalubale za a ce kin fuskanta a cikin gwagwarmayar rayuwarki?
To a gaskiya na fuskanci ƙalubalai da dama, wanda ba ma zai faɗu ba gaskiya, domin babu irin kallo ko suna da ba a kirani da shi ba, domin mu anan Ƙasar Hausa musamman a Jihar Jigawa da damawar mata a fanonnin da dama ya yi ƙaranci, gani ake idan mace tana shiga tana fita kamar wani abu rashin gaskiya take aikatawa, ni fa common sunanan yasa ana min kallon ni yare ce, ko abu nayi sai a ce ai ni ba bahaushiya ba ce yaushe nasan Hausa, ko lokacin da na fara rubuta littafin yadda kasan mahaukaciya haka ‘yan gidanmu da al’umma suke kallona, sunce kawai vata lokaci na nake, amman babu inda littafina zai je, amman ban damun ba, domin komai na da lokaci, kamar yadda lokaci yake nunawa.

Za ki iya faɗa mana nasarorin da kika samu?
A gaskiya na cimma nasarori da dama wanda a shekaruna gaskiya sai dai kawai a ce alhamdu lillahi ala kulli halin, ko mai masters albarka. Babban burina a rayuwa shine na zama babbar marubuciya, ‘yar kasuwa, kuma babbar ‘yar jarida.

Ki na da burin ci gaba da rubuta wasu littattafai?
Sosai Ina da burin ci gaban da rubuce-rubuce. Akalla littatafan da na rubuta sun kai biyar zuwa 6, kuma ina da burin su zama da yawa, infact su cika half library. Domin ina so ko bayan raina littafina yana faɗakar da al’umma, sannan ya kasance wani forum da mutum zai iya lalubo maganin damuwarsa.

Da ya ke ki na aiki a gidan rediyo. Kina da burin aiki a manya kafafen kamarsu BBC da sauransu?
Hmmm, har ka ba ni dariya, dama ɗaya ce ta ke zuwa a rayuwa, wato ‘opportunity cames once in life’, Don haka idan dama ta zo ma ka, ka dama da ita a wannan lokaci da ta same ka. Ina da sha’awar zama ma’aikaciyar irin waɗannan gidajen rediyon sosai, amma so ba samu ba ne. Amman Allah ya tabbatar da alkhairansa da na fi kowa farin cikin.

Wacce shawara kike da shi ga ‘yan uwanki matasa?
Shawarar da nake da ita zuwa ga matasa ‘yan’uwana shi ne, duniya bata auran rago kuma babu maraya sai rago, karka dubi ƙarancin karatu ko ƙarancin shekarunka, kawai ka tashi ka nema domin mai neman na tare da samu. A matsayinka na matashi ko matashiya ku zama waɗanda za a yi kwatance dasu, domin idan muka dosa yana nuni da su waye a gabanka kafin kai. Dan haka mu zama nagari domin na ƙasa suma su zama nagari.

Madalla. Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.