Fa’idar Habbatus Sauda (2)

Tambaya:
Anti Bilkisu, mu na son mu san falalar Habbatus-Sauda.

Amsa:
Habbatus Sauda kwaya ce mai albarka wadda take tattare da fa’idoji kala-kala a jikin ɗan’adam wanda ya kamata dukkan iyali ya kyautu a ce suna ajiye ta a cikin gida domin magani da kariya ga iyali da kiwon lafiya.

Ana kiran habbatus-sauda da sunaye daban-daban saboda muhimmancinta da shahararta. Bayan sunanta habbatus sauda ana kiranta Habbatul Baraka. Da Turanci kuma ana kiran ta da blessed seed, Black cumin, Nigella sativa , black caraway da sauransu.

Ga mai fama da larurar tsakuwar ƙoda a sami zuma mai kyau a sami garin habbatus sauda a cuɗe su a ke shan babban cokali sau biyu a rana.

Wanda yake ciwon kai sai a sami habbatus sauda ta gari a cuɗe ta da ma’u khal tuffa a ke shafa wa a goshi sau uku sannan ana ɗigawa a hanci.

Man habbatus sauda yana magance larurar ciwon kunne ana haɗa shi da man zaitun ake ɗiga wa a kunne.

Ga mai larurar shafar shaiɗanu ana amfani da man Habbatus sauda a rinƙa sha ana shafe jiki da shi.

Yin turare da kwayoyin habbatus sauda yana korar shaiɗanu a wuri.

A samu garin habbatus sauda a haɗa da garin tafarnuwa da cutta kaɗan da zuma mai kyau a cuɗe su ake shan babban cokali ɗaya kullum wannan yana magance larurar sanyi ko mura wadda ta daɗe a jiki.

Ga wanda cikinsa yake yawan kumbura musamman yara yana da kyau ake ba su man habbatus sauda kaɗan suna sha.

Fa’idojin Habbatus sauda manta da garinta ba za a iya faɗarsu ba duka sai dai a tsakuro wanda za a iya. Abin nufi dai ya kamata a ce kowanne gida akwai habbatus sauda don tana da muhimmanci kwarai a zamantakewar iyali.

Ga mai neman ƙarin bayani ya turo saƙon tes a wannan layin ko ta whatsup a lambar 07088683334 ko a duba shafin Facebook ɗina mai suna Bilkisu Yusuf Ali