Ku zaɓe ni don inganta cigaban Neja, Malagi ga daliget na APC

Daga BASHIR ISAH

Mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja kuma na kan gaba daga jerin ‘yan takarar gwamna a Jihar Neja ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya yi kira ga daliget na jam’iyyarsu a jihar da su zaɓe shi a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar na APC a zaɓen fidda gwanin da zai gudana yau Alhamis a Minna.

Malagi ya yi wannan kira ne sa’ilin da yake ganawa da manema labarai dangane da takararsa ranar Laraba a Minna, babban birnin jihar.

Ɗan takarar ya ce, “Na yi alƙawarin sake bunƙasa Jihar Neja muddin aka zaɓe ni a matsayin gwamnan jihar a 2023, wanda zama gwamnan ba zai yiwu ba sai idan daliget sun amnince sun zaɓe ni a zaɓen fidda gwani.

“Don haka nake kira ga daliget ɗinmu da su ba ni wannan dama na zama ɗan takarar gwamna a APC,” inji shi.

Daga nan, Kaakaki Nupe ya ce idan ya zama gwamnan jihar zai bai wa fannin tsaro da kuma bunƙasa muhimmanci.

Ya ƙara da cewa, “Gwamnatinmu za ta tabbatar da ta farfaɗo da harkar noma a jihar wadda ita ce sana’ar da aka san al’ummar jihar da ita don ƙarfafa tattalin arzikin jihar.

“Za mu tabbatar da harkar noma ta samu tagomashi yadda ya kamata, za mu yi aiki tukuru wajen inganta tattalin arzikin jihar. Sannan za mu tabbatar da mun raba matasanmu da zaman kashe wando.”

Malagi ya nuna takaicinsa dangane da ƙalubalen tsaron da Jihar Neja ke fuskanta, wanda a cewarsa matsala ce babba wanda ya kamata a yi amfani da takalmin ƙarfe wajen take ta.

“Abin baƙin ciki da damuwa ne ganin yadda matsalar tsaro ta raba wasu al’ummar jihar da matsugunnansu,” inji shi.

Daga nan, ya shawarci ‘yan jarida da su guji yaɗa labaran ƙarya a harkokinsu, yana mai cewa labarum ƙarya na kisa.

Ya kuma nuna damuwarsa a kan yadda wasu kan zauna su ƙirƙiri labarum ƙarya sannan su yaɗa a cikin al’umma wanda a cewarsa, hakan ba daidai ba ne.

Ya ce dole a san cewa sai da zaman lafiya jihar za ta zauna ƙalau ta bunƙasa a yau da kuma gobe.