Daga CMG HAUSA
Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta fada Juma’ar nan cewa, jawabin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi kan manufofin ƙasar Sin, ya yada labaran karya a cikinsa, ya kuma azuzuta wai “barazanar ƙasar Sin”, da tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasar Sin da kuma bata sunan manufofin cikin gida da waje na ƙasar Sin.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa taron manema labarai cewa, ƙasar Sin ta nuna rashin amincewarta da ma adawa da kakkausar murya kan wannan jawabi.
Wang ya ƙara da cewa, sakatare Blinken ya bayyana cewa, Amurka ba za ta nemi rikici ko tayar da wani sabon yaƙin cacar baka da ƙasar Sin ba, kuma tana son zama lafiya da ƙasar Sin, za mu jira mu gani.
Ya kuma lura da cewa, Amurka tana iƙirarin cewa, ƙasar Sin ita ce babban ƙalubale ga tsarin kasa da kasa na dogon lokaci, Yana mai cewa, a matsayinta na ƙasar da ta tsaya tsayin daka wajen kare tsarin ƙasa da ƙasa, kullum ƙasar Sin tana nacewa wajen ganin cewa, ya kamata dukkan ƙasashe su martaba tsarin ƙasa da ƙasa tare da MƊD a matsayi jagora, da tsarin ƙasa da ƙasa bisa dokokin ƙasa da ƙasa, da kuma muhimman dokokin tafiyar da dangantakar ƙasa da ƙasa bisa manufofi da ƙa’idojin yarjejeniyar MƊD.
Daga nan Wang ya yi nuni da cewa, ƙasar Sin ta yi imanin cewa, kamata ya yi hulɗar dake tsakanin kowace ƙasa ta kasance bisa daidaito, da tuntuɓa, da fahimtar juna, kana ya kamata dukkan ƙasashe, su daidaita makomar duniya tare. Tsarin haɗin gwiwar kasashen dake yankin tekun Indiya da Pasifik da Amurka ta ƙaddamar wani salo ne na kafa wani gungu, wanda kuma ba zai taɓa yin nasara ba.
Fassarawa: Ibrahim
