Yaya Ƙasar Sin take a sabon zamani? Waɗannan sababbin fina-finai sun fayyace amsa

Daga CMG HAUSA

Yaya ƙasar Sin take a sabon zamani? Jerin shirye-shiryen da babban gidan rediyo da talabijin na ƙasar Sin wato CMG a taƙaice ya shirya kwanan baya, dangane da “Ƙasar Sin a Sabon Zamani” irin su “Yadda ƙasar Sin take a shekaru goma da suka wuce”, da “Labarun ƙasar Sin a idona”, da “hanyar samun wadata tare”, sun ba ku labaran abubuwan da suka faru a ƙasar Sin cikin shekaru goma da suka gabata.

Baya ga shirye-shiryen da aka ambata a baya, an ƙaddamar da “bikin bidiyo na ƙasar Sin”, wanda CMG da ma’aikatar al’adu da yawon buɗe ido ta kasar Sin suka shirya a hukumance, a kwanaki kaɗan da suka gabata.

Ya zuwa yanzu, gidajen talabijin, da cibiyoyi na ƙetare guda 30, daga ƙasashen Afirka 20 ne suka halarci wannan baje kolin, kuma za a nuna shirye-shiryen bincike masu inganci na ƙasar Sin fiye da 50, wanda gidan talabijin na CGTN, dake ƙarƙashin jagorancin CMG ya shirya a ƙasashen ƙetare ɗaya bayan daya, wanda hakan ke haskaka gaskiyar ƙasar Sin a dukkan fannoni ga abokai na Afirka.

Mai fassara: Bilkisu Xin