Kamfanonin Ƙasar Sin sun shirya taron horar da matasan Afrika

Spread the love

Daga CMG HAUSA

An buɗe cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire da ilimin zirga-zirgar jiragen ruwa ta farko, ƙarƙashin jagorancin kamfanonin ƙasar Sin, jiya Alhamis a birnin Djibouti City na ƙasar Djibouti.

Taken cibiyar shi ne, ƙirƙire-ƙirƙire na zamani da cinikayya ta intanet tsakanin ƙasa da ƙasa.

Kusan mutane 30 daga ƙasashen Djibouti da Habasha da Kenya da Uganda ne aka zaba domin su karɓi horon na kwanaki 8.

Kuma yayin horon, matasan za su koyi darussan tafiyar da harkokin kamfani, kana za a gabatar da lokaci da tarukan ƙara wa juna sani daga masanan Sin da Afrika tare da ziyartar tashar jiragen ruwa ta Doraleh da yankin cikin cikin ’yanci na ƙasa da ƙasa na Djibouti da kamfanonin ƙasar Sin suka gina.

Cibiyar da aka kafa ba don riba ba, na da nufin inganta bunƙasa ƙwarewar matasa da dabarun shugabanci da ilimin sana’o’i tsakanin matasan Djiboutu da na gabashin Afrika.

Haka kuma za ta bayar da gudunmawa ga burin da Djibouti ke son cimmawa zuwa 2035, domin bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire a ɓangarori masu zaman kansu da dogaro da kai.

Cibiyar wadda ’yan kasuwar ƙasar Sin suka samar da kuɗin kafa ta yayin da ƙungiyar ’yan kasuwar Sin dake Djibouti ke tafiyar da ita, za ta zama dandalin samar da hidimomi kamar na horo da bayar da shawarwari da hada ’yan kasuwa.

Mai Fassarawa: Fa’iza Mustapha

By Editor