Daga IBRAHIM YAYA
Galibi ana kafa asusu ne da nufin inganta fannoni na ilimi ko harkokin ci gaban mata da ƙananan yara ko raya harkar lafiya da agazawa waɗanda bala’o’i suka shafa da makamantansu.
Kamar sauran irin waɗannan asusu da kasashe ko al’ummomi ko ƙungiyoyi masu zaman kansu ke kafawa, shi ma asusun raya yankunan karkara na ƙasar Sin ko CFRD a takaice, ya amsa manufofin kafa shi, duba da irin managartan ayyukan da yake gudanarwa a ciki da wajen ƙasar.
Ayyuka na baya-bayan da asusun ya gudanar a ƙasar Habasha, ya samu yabo da jinjina, a daidai lokacin da aka yi bikin cikarsa shekaru 3 da buɗe ofishinsa a ƙasar ta Habasha.
Shi dai asusun ya fara gudanar da ayyuka daban-daban a Habasha tun daga shekarar 2015, an kuma yi masa rajistar gudanar da ayyuka a matsayin asusun ba da tallafin jin kai na ƙasa da ƙasa a ƙasar a watan Yulin shekarar 2019, inda ya karkata ga zurfafa haɗin gwiwar musaya tsakanin al’ummun Sin da na ƙasar Habasha.
Bayanai na nuna cewa, asusun CFRD ya shafe shekaru 7 yana gudanar da ayyuka daban-daban a Habasha, ciki har da ciyar da ɗaliban makarantu, da raba kayan karatu, da kayan abinci, da ruwan sha da ayyukan tsaftar muhalli, da ayyukan bunƙasa tattalin arzikin mata, ayyukan da suka amfani sama da ’yan ƙasar Habashan 250,000.
Haƙiƙa ayyukan asusun CFRD, sun yi daidai da muhimman ayyukan da gwamnati da al’ummun Habasha ke bukata, waɗanda ke da matukar tasiri ga ci gaban ƙasar.
Sabanin yadda wasu ƙasashen yammacin duniya ke kafa asusu da sunan raya demokuraɗiyya ko Ilimi ko wasu ɓangarori na rayuwa, amma suke fakewa da hakan wajen tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasashe da ma neman shafa musu baƙin fenti ko hana ci gabansu.
Wannan ne ma ya sa babban daraktan ƙungiyoyin masu zaman kansu na ƙasar Habasha Jima Dilboi ya yi kira ga asusun na CFRD, da ya jagoranci ƙungiyoyi masu zaman kansu dake Habasha, wajen ƙulla alaƙa da sauran ƙungiyoyi da hukumomi na ƙasa da ƙasa, kamar shirin samar da ci gaba na ƙasa da ƙasa, da na hadin gwiwar bunƙasa ƙasashe masu tasowa, da shirin ziri ɗaya da hanya ɗaya.
A daina fakewa da guzuma ana harbin karsana.
