Aikin jarida ya ba ni damar faɗakar da jama’a – Halima Ben Umar

“Shirin ‘Mata A Yau’ ya canza rayuwar iyalai da dama”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Sunan Hajiya Halima Ben Umar ba ɓoyayye ba ne a gidaje da dama na Nijeriya da maƙotan ƙasashe, musamman inda ake amfani da harshen Hausa, saboda rawar da ta ke takawa wajen gabatar da shirin ‘Mata A Yau’, wanda tashar talabijin na Arewa 24 ke gabatarwa. Tsohuwar ’yar jarida, ýar gwagwarmaya, kuma uwa, wacce gudunmawarta a harkokin cigaban al’umma ya ratsa birane da ƙauyuka, kuma har yanzu ta ke nuna kishi da jajircewa wajen faɗakar da ýaýa mata muhimmancin inganta rayuwarsu da ta iyalinsu. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya tattauna da wannan jajirtacciyar mace, wacce kuma ta shafe akasarin shekarunta wajen ilimintar da jama’a da yi musu hidima. Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance:

BLUEPRINT MANHAJA: Mu na son mu fara da jin wacce ce Halima Ben Umar?


HAJIYA HALIMA:To, ni dai sunana Halima Ben Umar. Kuma an haife ni ne a Unguwar Kankarofi, kusa da Gidan Sarki da Gidan Gyaran Hali na Kano. Na yi karatuna na firamare a Gidan Makama, daga nan na je makarantar firamare ta kwana da ke Shekara. Daga nan kuma na tafi Kwalejin ‘Yan Mata ta Gwamnati da ke Dala.

Bayan na gama Dala sai na tafi Kwalejin Nazarin Ilimin Addinin Musulunci ta CAS. A lokacin Ina da aure, sai maigidana ya ce, ya fi son aikin koyarwa, don haka daga bisani na shiga wata Kwalejin Nazarin Aikin Koyarwa ta ‘Pivotal’ wacce makaranta ce ta horar da waɗanda ba su samu horo kan koyarwa ba.

Daga nan kuma sai muka tafi Ƙasar Amurka, inda muka shafe wasu shekaru kafin nan muka dawo. Sai na koma makaranta, inda na koyi ilimin fasaha da ƙirƙira, wato Arts and design. Bayan na gama ne sai na samu aiki da Hukumar Bunƙasa Ayyukan Gona da Raya Karkara ta KNARDA.

Na yi aiki a KNARDA har zuwa 1999, daga nan ne kuma na samu aiki a Hukumar Raya Ƙasashe ta Gwamnatin Amurka wacce aka fi sani da USAID, inda muka riƙa gudanar da ayyukan raya ƙasa da cigaban al’umma, wanda Gwamnatin Amurka ke ɗaukar nauyi har zuwa shekarar 2003. 

Daga bisani na koma karatu a wata Jami’ar Ƙasar Amurka, inda na yi karatu na tsawon wata goma. Bayan na dawo sai na sake samun aiki na wani aikin da Hukumar USAID ke gudanarwa. Daga nan na aiki da wata ƙungiyar da ke aiki kan inganta rayuwar al’umma ta DFID (FCDO), har zuwa 2017.

Har wa yau na shiga shirin Open Government Partnership (OGP) wanda shi ma shiri ne na haɗin gwiwar gwamnati da ƙungiyoyin farar hula, don samar da ayyukan ci gaban al’umma. Na zama ni ce mace ta farko da ta riqe shugabanci kujerar haɗin gwiwa daga ɓangaren ƙungiyoyi masu zaman kansu, yayin da Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya zama shugaba da ke wakiltar gwamnati. Na kuma kasance Darakta a ƙungiyar mata ýan jarida da masu ayyukan sadarwa ta Women in Media Communication Initiative (WIM) wacce aka kafa ta tun 2000.

Ko za ki iya tunawa da gwagwarmayar da ki ka sha lokacin karatu?

Gaskiya na sha wuya musamman a jami’a, inda wasu malamai suka ba mu maimaita kwas wato carry over ni da wata abokiyar karatuna, yayin da wani kuma ya riqa ɗora min nauyin da bai kamata ba, yana damu na da na saya masa abubuwa masu tsada irin gwal da manyan turare, duk don neman tsira da mutunci da gama karatu lafiya. Sannan ga kuma yajin aikin ƙungiyar malamai ta ASUU shi ma ya sa ni cikin matsala sosai.

Yaya ki ka samu kan ki a matsayin ýar jarida?

Aikin da nake yi a KNARDA da kuma ƙalubalen da na fuskanta wajen zamantakewa da abokan aiki maza, ya sa maigidana ya bani shawarar komawa karatu, inda na je Jami’ar Bayero ta Kano wato BUK na yi digiri a ɓangaren aikin jarida. Bayan na kammala ne sai aka mayar da ni sashin watsa labarai na Hukumar KNARDA, sannan kuma lokaci zuwa lokaci Ina zuwa tashar Rediyon Kano Ina karanta musu labarai. Wannan shi ne mafarin shiga ta aikin jarida. 

Wacce gudunmawa ki ka bayar wajen ƙarfafa gwiwar mata a harkar aikin jarida?

Na bayar da gudunmawa mai yawa, kuma har yanzu Ina kan bayarwa, musamman a ɓangaren ba da horo da wayar da kai ga matasa ýan jarida. Sannan kuma duk inda aka samu dama Ina faɗakar da mata ýan jarida kan nauyin da ke kansu. 

Wacce rawa mata ýan jarida ke takawa ga cigaban al’umma?

Suna ba da gudunmawa sosai wajen wayar da kan al’umma, musanman mata da matasa, wajen al’amuran da suka shafi yau da kullum. Misali, ƙungiyar mata ýan jarida ta NAWOJ ta kan samu tallafi daga ƙungiyoyin da ke ɗaukar nauyin gudanar da wasu ayyuka musanman waɗanda za su amfanar da rayuwar mata da matasa. A cikin ‘yan jarida mata, muna da editoci da yawa, masu tsara shirye shirye, masu gabatar da shirye shirye da karanta labarai da yawa, har ma da shugabanni a ɓangaren gudanarwa. 

Tsakanin aikin jarida da koyarwa wanne ya fi baki damar ba da gudunmawar da ki ke so ga al’umma?

Gaskiya aikin jarida shi ne ya fi bani damar kusantar jama’a da faɗakar da su muhimman abubuwan da ya kamata su sani. 

Yaya aka yi ki ka samu kan ki a matsayin ɗaya daga cikin masu gabatar da shirin ‘Mata A Yau’ na tashar Arewa 24?

Nema na aka yi daga tashar Arewa24 aka ce in je na shiga cikin waɗanda za a tantance don gabatar da wani sabon shirin da ake so a fara. Kuma cikin ikon Allah da na je sai Allah ya ƙaddara zan zama ɗaya daga cikin masu gabatarwa.

Wanne tasiri za ki iya cewa shirin ‘Mata A Yau’ ya samu tsawon wannan lokaci?

Gaskiya shirin Mata A Yau ya yi tasiri ƙwarai ga rayuwar mutane, wanda duk inda muka shiga sai dai ka ji ana ta yi mana godiya, Sannan wata gagarumar nasara da zan ce shirin yana samu shi ne ta wajen canza rayuwar mutane.

Don akwai wani mutum da ya kawo mana ziyara yana tabbatar mana da cewa, ya shafe tsawon shekaru yana shan giya tun da ya zama saurayi, yanzu shekarunsa 63, amma ta dalilin kallon shirin ‘Mata A Yau’, ya shiryu ya daina shan giya, kuma idan ya tashi daga aiki kai tsaye yake wucewa gida.

Ya ce, yana sauraron shirinmu ya fahimci akasari matsalolin da yake fuskanta a gida shi da iyalinsa laifin sa ne, don haka ya samu matarsa ya bata haƙuri, sun fahimci juna, sun kuma yafi juna bisa saɓanin da suka riƙa samu a baya.

Yanzu sun koma zaman su lafiya, babu wata damuwa. Ni ko daga kan wannan ma zan iya cewa mun yi nasara sosai, wajen gyara rayuwar auratayyar wasu iyalai. 

Yaya batun ƙalubale, musamman bayan bayyanar bidiyon da aka riƙa yawo da shi a kafafen sadarwa na zamani?

E, a gaskiya ban ji daɗi ba sosai. A farko na so na ɗaga hankalina a kai, amma iyalina da iyaye da sauran masoya har da wasu ma da ban san su ba, sun yi ta ban baki da fahimtar da ni yadda har na samu sanyi a zuciyata.

Ni na san cewa, duk ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, kuma abin da ake yaɗawa mun yi ba fasiƙanci muka yi. Amma yadda wasu suka ɗauki abin har suna yaɗawa da faɗar maganganu marasa daɗi shi ne ya fi min zafi. Musamman shi wannan almajirin da ya yi ta aibata mu, ni na san na haife shi, in ma ban haife shi ba na yi sa’a da uwar sa.

Amma ya shiga wajen karatu yana mana cin mutunci. Na so idan da har ga Allah gyara yake so ya yi mana, zai iya zuwa inda muke ya yi mana nasiha, mu gyara inda muke kuskure, don amfanin jama’a. Amma shi ba haka ya yi ba, ni dai na faɗa masa ban yafe ba, kuma na bar shi da Allah ƙazafin da ya yi mana. 

Wacce matsala ki ka fuskanta game da iyalinki, a sanadiyyar wannan bidiyon?

Kamar yadda na gaya maka ban samu wata matsala da iyalana ba, ko kaɗan. Muna da kyakkyawar fahimtar juna, kuma tsakanin mu da su addu’a ce a kullum ta fatan gamawa da duniya lafiya. 

Kin taɓa nadamar wani abu a aikin da ki ke yi?

Gaskiya ban taɓa yi ba, saboda duk abin da zan yi, sai na gayawa Ubangiji, na kuma roƙe shi don ya yi min jagora!

Ba mu labarin rayuwarki ta aure, kina wanne shekara ki ka yi aure, kuma kawo yanzu yaranki nawa?

Anyi min aure Ina da shekara 16, kuma rayuwar aure na alhamdulillah. Duk abin da na zama, ba don da goyon bayan mijina da iyayena ba, gaskiya babu inda zan je. Kuma har yanzu duk in da zan je sai na nimi izinin mijina, ni na ke mishi abinci da sauran buƙatunsa.

Ina da yara 12, amma guda 7 ne wanda ni na haifa da kaina. Yanzu shekara biyu kenan da rasuwar yarona na 5, wanda Allah ya yi masa rasuwa a ranar da ya cika shekaru 25 a duniya.

Yaya ki ke haɗa ayyukan ki da tafiyar da iyalinki?

To, a gaskiya aiki ne mai wuyar gaskiya, saboda ɗawainiyar kula da gida da ta maigida da fita aiki ko karatu, ba abu ne mai sauƙi. Sai dai mun gode da muka kawo wannan lokaci, saboda goyon baya da tallafin da na samu daga maigidana, kakata da mahaifina. Allah ya jiƙan su da rahama. Sun taimaka min ƙwarai da gaske, domin ganin na samu sauƙin tafiyar da harkokina da tarbiyyar yara.

Musamman kakata ta ke zuwa gidana ta kula da yarana, idan ba na gida, saboda tsaurin da ta ke da shi a kan tarbiyya, duk da muna da masu aiki a gida, amma ba mu yi sake da batun tarbiyyar yaranmu ba. Ban yarda in bar wa mai aiki nauyin tarbiyyar yarana ba.

A haka dai aka yi ta bugawa, da daɗi da ba daɗi, rayuwa ta koya min yadda zan tsara abubuwana su tafi yadda nake so cikin sauƙi, har na kawo lokacin da na daina haihuwa, sai al’amarin tarbiyya da ba a gamawa. 

Wanne darasi za ki iya cewa rayuwa ta koya miki?

Zamantakewata da ýan’uwana mata, musamman wasu ƙawaye da na amince musu, suka je suka yi min ƙarya a wajen wata yayata da maigidana, abin da ya yi matuƙar ƙona min rai, kuma na koyi wani darasi na zaman rayuwa. Don tun daga lokacin na canza yadda nake mu’amala ta da mutane.

A matsayin ki ta ɗaya daga cikin taurarin mata na Arewa, wacce shawara ki ke da shi ga matasan mata da ke koyi da ku?

A kullum na kan gaya musu da su nemi na kansu, su koyi sana’a don yanayin halin da tattalin arziqin ya shiga wani hali, lallai ne matasa su samu abin yi kar su dogara sai ai an basu. Kuma mai ja musu hankali da su zama masu biyyaya ga mazajen su. Idan suna biyyaya to, in sha Allah za su samu kulawa a wajen mazajensu.

Wanne abu ne ki ke so a riƙa tunawa da ke?

Faxin gaskiya a duk inda nake kuma a gaban kowa.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Karin maganar da na fi tunawa da ita ita ce, wacce mahaifina ya taɓa gaya min tun Ina ƙarama, ka rabu da kowa ka kama Allah. Duk abin da zan yi Allah kawai nake kallo ba wani mutum ba.

Na gode.

Ni ma na gode ƙwarai.