Marubuci na iya saka rigar kowa ta zauna daram a jikinsa – Hassana Matazu

Haɗakar marubuta za ta ɗaga darajar adabi”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Gamayyar wasu haziƙan marubutan adabi su goma da suka ƙulla ƙawancen aikin rubuta wani littafi mai suna ‘Da Jininsa A Jikina’ na ci gaba da samun nasara a aikin da suka sa a gaba, na kafa tarihi da farfaɗo da kasuwar littattafan adabin Hausa. A yayin da aiki ke tafiya cikin salon jan hankali da nuna ƙwarewa ta ma’abota fasaha da sarrafa harshe, marubutan da ke aikin na sa ran nan da ƙarshen wannan shekara bugaggen littafin zai shiga hannun masu karatu. Ɗaya daga cikin marubutan wannan tauraron littafi ita ce, Hassana Suleiman Isma’il, da aka fi sani da Sanah S. Matazu, wacce ta kasance fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa da gajerun labarai ce, kuma ɗaya daga cikin fitattun marubuta mata a gasar Hikayata ta BBC Hausa na tsawon shekaru uku a jere. Wannan marubuciya na daga cikin ƙalilan ɗin marubutan Hausa na zamani da Allah ya yi musu baiwar salon sarƙafa magana da rikita ƙwaƙwalwar mai karatu, kafin su warware duk wani ƙulli da suka yi cikin hikima da basira. Shafin Adabi na wannan mako ya nemi jin yadda Sanah Matazu ta samu kanta cikin ayarin waɗannan jajirtattun marubuta, da yadda gwagwarmayar ta a harkar rubutun adabi ta kasance tun tasowarta.

BLUEPRINT MANHAJA: Ina son mu fara da jin cikakken sunanki.

SANAH: Cikakken sunana shi ne Hassana Suleiman Isma’il. Amma an fi sani na da Sanah S. Matazu.

Ko za ki gaya a mana tarihin rayuwarki, a taƙaice?

A taƙaice ni haifaffiyar garin Kano ce. An haife ni a ƙaramar Hukumar Gwale, a Unguwar ƙofar Waika. Na yi karatuna na firamare a makarantar Sheikh Isyaka Rabi’u daga bisani na koma ƙofar Ruwa S.P.S. Sai kuma na wuce makarantar gaba da firamare a G.G.S.S Ɗanɗinshe. Sai dai bayan kammala karatuna na sakandire ban samu dama na cigaba da karatuna ba, saboda wasu dalilai. Amma na kasance mai matuƙar sha’awar rubuce-rubuce tun tasowata.

Yaushe ki ka fara sha’awar yin rubutun hikaya na labaran adabi?

Zan iya cewa na soma sha’awar rubutu ne tun daga makarantar firamare. Hakan ya samo asali ne da ƙaunar da nake wa ɓangaren karatun Hausa. Domin tun daga aji biyu na firamare ni ce nake fitowa gaban allo Ina yi wa ‘yan ajin mu karatu har zuwa aji shida.

Haka ma a matakin sakandire na ɗora da wannan karatu, kodayaushe ni ce mai karatu a gaban aji. Ba zan manta ba akwai wani malaminmu Malam Mansur Ibrahim, duk lokacin da ya yi mana rubutu a kan allo sai na ci gyaransa ta fanin wasali ko kuma tuntuɓen alli. Kai tsaye da ma “mayya” yake ce mini. A lokacin Ina aji biyar a firamare.

Ko za ki gaya min wanene wanda ya ɗora ki a hanya har ki ka zama marubuciya?

Nacin karatu shi ne maƙasudin kusancina da marubuta. Kusancina da marubuta shi ne dalilin fara rubutuna. Amma wanda ya saka ni a hanyar rubutu shi ne Nura Sada Nasimat tare da tagomashin wani aji da ake koyar da rubutu a farko farkon fara amfani na da yanar gizo. Idan ban manta ba Muhammad Lawan Barrister da kuma Muhammad Lawan PRP su ne malamai a lokacin.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai sun kai nawa, ba mu bayanin wasu a taƙaice?

Littatafaina za su kai guda 20. Akwai waɗanda na rubuta a manhajoji akwai kuma waɗanda na fitar da su a buge. Daga ciki akwai ‘Shi Ne Burina’, ‘Rabi’Atul Adawiyya’, ‘Sanadin Bodin’, ‘Yanar Gizo’, ‘Gimbiya Zajlat’, ‘Yar Kurma’,’ Yar Mafiya’, ‘Yar Fulani Ce’, ‘Mahaifiyata Ce’, ‘Nadamar Rayuwa’, ‘Matar Sadik’. Akwai kuma ‘Fitsarin Faƙo’, ‘Sarƙaƙiya Kaidinsu’, ‘Lefen Aro’, ‘Wata Mace’, ‘Yarda Ce Sila’ da sauran su dai.

Kamar shi littafin ‘Shi Ne Burina’, labari ne kan maraici da kuma gallazawar kishiyar uwa. ‘Rabi’Atul Adawiyya’ kuwa labari ne kan soyayya, sarauta da kuma sadaukarwa.

Akwai kuma ‘Sanadin Bodin’ wanda labari ne kan rayuwar ‘yan makaranta da kuma yanayin yadda wasu al’amura suke kasancewa a rayuwar makarantar kwana ta bodin. Labarin ya tavo abin da ya shafi mummunar ɗabi’ar nan ta neman jinsi.

Sannan shi littafin ‘Yanar Gizo’ na gina labarin sa ne kan yadda yanar gizo ta yi nasara wurin daqile wasu al’adu da kuma tarbiyyar bahaushe. Sakamakon wasu sabbin abubuwa da halaye marasa kyau da matasa ke yi ta dalilin zaurukan sada zumunta da mu’amalar su a yanar gizo.

Shi kuma littafin Yar Fulani Ce’ labari ne da ya tavo al’adun fulani da wasu irin cukurkuɗaɗɗun al’amura da suka gindaya tauraruwar mutuwa ta dinga walankeluwa a tsakanin wani ahali. Alhalin duk alhakin kisan na wuyan jarumar labarin ne, wato Mairo.

Shi kuwa littafin ‘Fitsarin Faƙo’ wanda na yi shi na sayarwa ne, yana Manhajar Bakandamiya. Labari ne da na yi nasara da shi a gasar GUSAU INSTITUTE 2020, wanda da ya qunshi ƙalubalen da muke ciki ta fuskar tsaro da kuma wasu sakayyayun ɗabi’u da almundahana na siyasar ƙasarmu.

Wanne salon rubutu aka fi sanin ki da shi?

Bai kyautu a ce marubuci yana da salon da kai tsaye za a iya cewa ga inda ya fi karkata ba, domin shi marubuci yana da fuskoki da yawa da a wani bigiren dole ta ke sa ya aro su ya saka domin samar da abin da zai gamsar da masu karatu. Don haka ba ni da tsayayyen salo, duk salon da na ga ya kamata na ja hankalin al’ummata da shi Ina ƙoƙarin kwatanta shi matuƙar bai taɓa mutunci da kuma addinina ba.

Waɗanne nasarori ki ka samu ta dalilin rubutun adabi?

Ba zan ce ban samu wasu nasarori ko ɗaukaka ba, kuma Ina godiya ga ubangiji matuƙa da gaske a kan haka. Nasarata ta farko a rayuwar rubutu shi ne da ubangiji ya ba ni dama da kuma ikon fara rubutu, domin shi ne abu mafi nasara da zan yi tinƙaho da shi.

Na soma cin gasa a gasar Tsangayar Marubuta a shekarar 2018 inda na samu zama ta uku da labarina mai suna ‘Kudkurena’. Daga nan sai gasa ta biyu da na samu nasara, wacce zauren Marubuta na manhajar WhatsApp ya shirya a shekarar 2019 shi ma na samu zama ta uku da labarina mai taken ‘Ɗiyar Mace’.

Sai kuma gasar Mujallar Zauren Marubuta ta shirya a 2019, inda na yi ta huɗu da labarina mai taken ‘Sakacinmu’. Daga nan sai gasa mafi ɗaguwar daraja a gareni, wato gasar Gusau Institute ta 2021 inda na samu zama ta farko a matsayin wacce ta lashe kambun. Ina alfahari da ita matuqa, domin ni ce mace ta farko da na ɗauki kambun saɓanin baya inda duk maza ne suke ɗauka. Na samu nasara ne kuwa da labarina mai taken ‘Fitsarin Faƙo’.

Sai kuma a gasar Hikayata ta marubuta mata wanda Sashin Hausa B.B.C ya shirya a shekarar 2020 inda labarina mai taken ‘Rayuwarmu’ ya samu zuwa mataki na 5 a cikin jerin fitattun labarai goma da aka shigar a gasar.

Ko a wannan shekarar ma na samu wasu nasarori da suka haɗa da gasar Minna ta The Nigeria Prize wacce na samu zama ta 3 da labarina mai taken ‘Sarƙaƙiya’. Sai kuma gasar marubuta ta Exquisite Compitition wadda aka yi akan Almajiranci ita ma na zo ta uku, da labarina mai taken ‘Gani Ga Wane’.
Baya ga haka kuma na samu takardun karramawa daga wuraren da ƙungiyoyi daban daban. Alhamdullilah.

Kina daga cikin marubuta goma da suke aikin rubuta littafin ‘Da Jininsa A Jikina’, wanne ɓangaren ki ke aiki a kai?

Tabbas Ina ciki, ɓangare kuma babu ɓangaren da babu ni a ciki, domin duk inda igiyar labarin ta zargo ta zarge ɗayanmu zai iya kasancewa mai mafita a hannunsa. Don haka kowanne ɓangare akwai hannuna a ciki.

Wanne abu ne ya baki ƙwarin gwiwar shiga wannan haɗaka?

Abin da ya ba ni ƙwarin gwiwa na shiga shi ne, ganin tarin haziƙan da aka tara a wurin kuma cikin hukuncin Allah sai ga ni tsulum a cikin su. Wannan ma ya ƙara mini ƙwarin gwiwa, domin ko babu komai dai an ce da kwana da jahili gara yini da malami!

Kina ganin wannan littafin yana da labari mai ƙarfin da zai ja hankalin masu karatu?

In sha Allahu Ina kyautata masa zato, domin daga yadda masu karatu suke ɗokin ganin fitarsa, hakan zai tabbatar maka da cewa akwai nasara.

Wanne darasi littafin ‘Da Jininsa A Jikina’ yake koyarwa?

Darasi…’Da Jininsa A Jikina’…Tab! Zan iya ce ma ka abu ne a dunƙule, ko kuma na ce ma ka mace ce ɗauke da ciki…Sai dai Ina da yaƙinin tauraruwarsa za ta zamo wata irin tauraruwa mai armashi da haskenta zai sake haskaka fuskar masu haske a tafiyar. Zai kuma fito da ƙima da mutuntakar zamowar wasu a cikin tafiyar.

Bangon littafin ‘Da Jininsa’

Yaya ki ke ganin irin wannan haɗaka ta rubutu za ta kawo cigaba a harkar rubutun adabi?

Tabbas hanya ce mai matuƙar amfani da za ta ɗaga darajar adabi zuwa bigire mafi ƙololuwa.

Kawo yanzu yaya aikin rubutun ke tafiya, kuma wacce nasara ko ƙalubale ake fuskanta?

Aiki na tafiya cikin karsashi da kuma nasara mai armashi ba tare da ginshira ba. To, ga mai rubutu ma kenan, ina kuma ga mai karatu?

Menene shawarar ki ga sauran marubutan da suke wannan aikin littafi?

Shawarata ita ce su yi haƙuri, su ari juriya su yafa su kuma saka naci wurin daddana sandarmu mu miƙar da ita zuwa bigiren da zai kyautata gobanmu.

Wanne abu ne wannan littafin zai zo da shi wanda babu irin sa a sauran littattafan Hausa?

Ɗingishin kwaɗo ne tafe da sawun keken da sai mai hankali kawai zai iya fuskanta.

Menene burinki nan gaba a matsayin ki ta marubuciyar labaran adabi?

Burina shi ne tabbatar da haɗin kai tsakanin marubutan Hausa, tare da asassa wata gidauniya da za ta iya zamowa abin dogaro ga matsalolin marubuta ba tare da rauninsu ya bayyana a idanun duniya ba. (harshen damo).

Wacce karin magana ce ta ke tasiri a rayuwarki?

Masu hikimar magana na cewa rubutunka kamanninka. Ni kuma na ce ko ɗaya ba haka ba ne, saboda marubuci kamar ɗan leƙen asiri ne yana iya saka rigar kowa kuma ta zauna daram a jikinsa ya yi wadaƙa yadda yake so!

Mun gode.

Ni ma na gode.