Gamayar ƙungiyoyin 1,000 NCPC ta yi babban taro a Kano

Manhaja logo
Spread the love

DAGA MUHAMMADU MUJJITABA a KANO

Shugaban gamayar ƙungiyoyin bunƙasa rayuwar al`umma ta fanin ilimi kiwan lafiya da sauransu, Malam Askiya Sheikh Nasiru Kabara, ya jagoranci gangamin taron ƙungiyar da ya gudana a birnin Kano, a ranar Lahadin makon jiya.

A jawabinsa ga mahalata gangamin ya ce, wannan ƙungiya an kafa ta ne domin talafawa ƙoƙarin hukumomi na bunƙasa harkar lafiya, ilimi, bunƙasa tattalin arziƙ, da sana oin dugaro da kai wanda aikin wannan ƙungiya zai bada gagarumar nasara wajen samar da zaman lafiya tsoro da kwanciyar hankali dama najeriya baki ɗaya kamar dai yadda shugaban wannad ƙungiya Malan Askiya ya bayana a wurin taron.

A ƙarshe ya ce, mahalata taron sun futo ne daga sassa daban daban na jahar kano da qasa kuma ya shawarcesu kan bin doka da oda ka kuma sadaukar da kai wajen tausayawa al`uma da taimakonsu ako wane lokaci.

By Editor