Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gidauniyar wayar da kai da cigaban Al’umma wato Faundation For Social Orientation and Gender Development (FOSOGED ta baiwa Yan mata 20 horo a kan naura mai ƙwaƙwalwa da ya gudana a Husna Plaza da ke unguwar Sharaɗa cikin Birnin Kano,
A Jawabinta shugabar Ƙungiyar Hajiya Mariya Durumin iya ta bayyana cewa sun shirya Bada hoton ne don qara ƙarfafar ‘yaya mata ta yadda duk wani vangare na cigaba a rayuwa su ma ya kasance su ma an dama da su musamman harkar fasahar sadarwa wanda a yanzu da shi ne duniya ta ke cigaba.
‘Muna ganin yanzu idan suka koyi ilimar na’urar mai ƙwaƙwalwa da taswira akan na’urar to sana’a ce da za su iya gudanarwa ko da a gidajen mazajensu ne suna yi suna samun alheri da ita, ba sai lallai mun ɗora tunanin yaranmu a kan cewa idan sun yi karatu sai sun yi aikin gwamnati ba” inji Hajiya Rabi.
Tunda farko a Jawabinsa tsohon shugaban hukumar Adaidaita ta jihar Kano, malami a Jami’ar Bayero kuma uban ƙungiyar Dr. Bala Muhammad ya bayyana cewa, waɗannan ɗaliban da suka ko yi kwamfuta kamar sadaka ce mai gudana ce ga shugabannin Gidauniyar da suka ɗauki nauyin xaliban da waɗanda suka koyar, da kuma su kansu iyayen da suka koyar da su.
Sannan ya yi kira ga ɗaliban cewa, “su kansu waɗanda ba su ci ba za su dawo su mai maita domin so ake ku ƙware don ku ma wata rana ku koyawa na ku ‘ya’yan”.
Sannan ya yi albishir da cewa nan gaba ƙungiya za ta koyar da ilimin rubutu da yadda ake yin magana da kuma har yadda ake yin fim mai ma’ana da zai amfanar da alumma.
Aisha Abubakar Hassan ta na ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da koyarwar ta ce, “na koyi abubuwa da yawa musamman ma wajen haxa memo da typing babu shakka ba abinda za mu ce sai Allah ya saka masu da alheri.
Taron dai ya samu halartar shugaban Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya Finafinan ta jihar Kano, Malam Ado Ahmad Gidandabino, da iyayen yaran da DPO Sharada, da manyan baƙi maza da mata.
