Dandalin shawara: Ba na sha’awar namiji sai mace ‘yar uwata

Data AISHA ASAS

TAMBAYA:

Good morning, my darling aunty Asas. How was your night? Sorry na yi kiran ki tun da safe, daga baya ƙawata ta ce, ai saƙo zan tura. Mun tava haɗuwa da jimawa, but I think you will not remember, saboda an jima, kan case na wata ƙawata da har ki ka je gidansu about her been raped. Yanzu ma wurinta na samu your number. Matsalata gaskiya I will be honest with you tun da mafita nake nema, wallahi ba na sha’awar namiji gabaɗaya, irin na fi feeling ina buƙatar mace idan na yi sha’awar abin, amma fa ban taɓa yi ba, kawai irin ko a mafarki da mace nake gani na, kuma idan na yi tunanin aure matuƙar na tuna da namiji zan zauna sai auren ya fice data raina. Ki taimaka min da shawara please don na fahimci kina da fahimta tun ma ga yadda kin yi depending friend ta a gaban iyayenta a nata case. What can I do, Aunty Asas?

AMSA:

Alhamdu lillah. Wataƙila kin gama ayyana yadda amo da sautin alƙalamina zai kasance a farko, takan yiwu kin sa wa ranki zan soma da karatun Bature da ya jima yana karantarwa kan sha’anin sha’awar jinsi ɗaya, inda yake son duniya ta amince yananyin halittar mutum ce mai zaɓen jinsin da zata yi sha’awa tsakanin nata da na ɓangare ɗaya. Da wannan suke ganin bai zama illa ko abin ƙyama ba ga wanda ya yi sha’awar irin jinsinsa.

Idan wannan ne ki ke fatan in fara shimfiɗa da shi, to fa zan ba ki kunya anan, domim ko kaɗan ban yarda da wannan kalaman ba bare har na karantasu ga wani. Sha’awa halitta ce mai zaman kanta a jikin ɗan Adam, kuma mahaliccinta ya yi ta ne tana kallon jinsin da ba nata ba, ma’ana ta jikin mace ta kwaɗaitu da jinsin namiji, haka shi ma tasa bata kallon kowanne jinsi da ba mace ba. Wannan ita ce sananniyar sha’awa ta tun ran gini.

Idan har aka wayi gari ta sauya kallonta zuwa ga jinsin da yazama ɗaya da mai ita, to fa lamari ne da ke da fuska biyu. Na farko ruɗin sheɗan wanda lokuta da dama ya fi rinjaye. Sai kuma wata matsala ta mutanen ɓoye da na ji malamai na maganar sha’awar jinsi na ɗaya daga cikin alamomin ta. Haka kuma sun bayyana ɗabi’ar a matsayin hanyar da ke ba wa sheɗanun aljanu dama ga kai wa ga jikin ɗan Adam.

Bari mu fara da na farko, wato ruɗin sheɗan. Wannan kan samu ne sanadiyyar kusanci da ya sava wa shari’a, abin nufi, addini ya gindaya iyaka da ya kamata balagagu biyu su tsaya ta ɓangaren kusanci. Idan na ce kusanci Ina nufin idan zama ya haɗa ku, ko ƙawance da jinsin da yake irin naki, kada ku ce ai duk abu ɗaya ne, ku dinga bayyana tsiraici a gaban juna, ko matse wa juna yayin kwanciya da makamantan ta.

Wannan na ɗaya daga cikin ɗabi’u da suka fi yawa a tsakanin mata, musamman idan ka tafi makarantun kwana na yara mata. Za ka tarar da ɗabi’u da dama da Musuluci ya haramta, kamar wanka tare, za ka ga baligu sun tuve gaban juna suna wanka, ko wurin kwanciya a manne juna da sunan jin sanyi ko wuri ya yi ƙaranta. Waɗannan na daga cikin hanyoyin da sheɗan ke bi wurin dasa sha’awar jinsi.

Idan muka yi duba da shekarun matan da ke matakin sakandare, za mu tarar sun kai munzalin samun tsiron sha’awa, kuma kamar yadda muka faɗa a wani darasi a baya, sha’awa halitta ce da ta bambanta a jikin ɗan Adam, wata na da kaɗan yayin da wata da yawa, kamar yadda malamai suka ce ta kasu kashi uku, akwai ‘kharija’, wato wadda ke da ƙololuwar sha’awa da ba a cika iya gamsar da ita ba. Ita mai wannan nau’in sha’awa abu kaɗan zai iya tada ita, wanda kusanci sosai na ɗaya daga ciki.

Ire-irensu ne ya kamata iyaye su rage dogon buri na karatu kansu har sai bayan aure, domin da yawa daga cikin su ne ke ajiye kunya su nemi iyayen nasu su masu aure. Kawar da kai daga gare su na ɗaya daga cikin dalilan da ke jefa waɗansu ga zina ko sha’awar jinsi.

Kashi na biyu kuwa ana kiranta da ‘mutawasiɗa’, wato matsakaiciya, ita ba ta kai ta farko ba, sannan ba ta cikin nau’i na uku da za mu faɗa. Ita ma ta kan samu kanta a matsala yayin da ta buƙaci aure, ma’ana tana da ƙarfin sha’awa duk da ba ta kai ta farkon ba.

Ta ƙarshe ita ce, ‘dakhila’, ita mace da ke kan wannan matsayi ko namijin da yake wannan vangaren su ne ake wa kallon marasa lafiya a wasu lokuta, ba wai ba su yi ba kwata-kwata, sai dai abin bai dame su ba. Don haka ba su samun kansu a tsangwama ta sha’awa har su kai ga aikata ɓarna.

Za mu ci gaba mako mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *