Ƙungiyar nan mai rajin a yi aiki da gaskiya da aka fi sani da SERAP a taƙaice, na zargin gwamnonin jihohi 36 kan rashin bada cikakken bayani game da yadda suka sarrafa Naira biliyan 72 da aka ba su a matsayin tallafin rage raɗaɗin cire tallafn fetur da gwamnati ta yi.
Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi ta bakin Daraktanta, Kolawole Oluwadare, ƙungiyar ta ce ta shigar da ƙara a kan gwamnonin, tare da neman cikakken bayani daga gare su game da waɗanda aka tsara su ci gajiyar shirin da kuma kayayyakin da suka saya da kuɗin da aka ba su.
A baya-bayan nan Gwamnatin Tarayya ta raba wa jihohin kuɗi Naira biliyan bibbiyu a matsayin ɓangare na biliyan biyar-biyar da ta ware wa kowace jiha don rage raɗaɗin cire tallafin fetur.
Ƙarar mai lamba FHC/L/CS/1943/2023 wadda aka shigar a Juma’ar da ta gabata a Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, SERAP ta nemi kotu ta bai wa gwamnonin jihohin ƙasar nan 36 umarnin kowannensu ya fito ya yi bayanin yadda ya kashe biliyan biyun da aka ba shi don amfanin talakawansa.
Kazalika, ƙungiyar ta nemi kotu da ta bai wa gwamnonin umarni a kan su bai wa ICPC da EFCC odar su sanya ido kan yadda suka kashe kuɗaɗen tallafin da aka ba su, da dai sauransu.
Kawo yanzu dai ba a tsayar da ranar da kotun za ta fara sauraren ƙarar ba.
Rahotanni daga sassan ƙasa sun nuna yadda jama’a suka yi ta ƙorafi game da kayan abincin da gwamnatocin jihohi suka raba musu da sunan tallafin rage raɗaɗin cire tallafin fetur.
