An yi jana’izar mahaifiyar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Hajiya Halima

Spread the love

An yi jana’izar mahaifiyar tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan; Hajiya Halima (Dada) wadda Allah Ya yi wa rasuwa garin Gashuwa, shalkwatar ƙaramar hukumar Bade a jihar Yobe.

Taron jana’izar ya samu halartar dandazon jama’a daga sassa daban-daban daga ciki da wajen Jihar Borno.

Mahaltar sun haɗa da Gwamnan Jihar Yobe, Farfesa Babagana Umara Zulum da Mataimakinsa, Idi Barde Gubana da sarakuna da sauransu.

Sanata Lawan ta bakin kakakinsa, Ezrel Tabiowo, ya yi godiya ga ɗimbin jama’ar da suka halarci taron jana’izar.

By Editor