Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tsige shugabanni wasu hukumomin gwamnati ƙarƙashin Ma’aikatar Yaɗa Labarai.
Kakakin Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, shi ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta nuna tsigewar ta shafi shugabannin hukumomin NOA da FRCN da NBC da dai sauransu.
Haka sanarwar, ta ce Tinubu ya baɗa sabbin shugabanni da za su maye huraben waɗanda aka tsige.
Ga sabbin naɗe-naɗen kamar haka:
1) Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) — Mr. Lanre Issa-Onilu
(2) Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA) — Mr. Salihu Abdulhamid Dembos
(3) Tashar Rediyo ta Tarayya (FRCN) — Dr. Muhammed Bulama
(4) Hukumar Kula da Kafofin Yaɗa Labarai (NBC) — Mr. Charles Ebuebu
(5) Muryar Nijeriya (VON) — Mr. Jibrin Baba Ndace
(6) Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Ƙasa (ARCON) — Dr. Lekan Fadolapo
(7) Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) — Mr. Ali Muhammed Ali
(8) Cibiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NPC) —Mr. Dili Ezughah
