Da Ɗumi-ɗumi: Ƙanin Sarkin Zazzau, Mansur Nuhu Bamalli ya kwanta dama

Spread the love

Sanarwar da mai magana da yawun Masarautar Zazzau ya fitar ta ce marigayin ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa a Legas a hanyarsa ta zuwa ƙasar Moroko.

“Za a sanar da lokacin da za a yi jana’izarsa nan gaba kaɗan,” in ji sanarwar.

Ya rasu yana da shekara 52, sannan ya bar mata guda da ‘ya’ya biyu.

Kafin rasuwarsa, Mansur Nuhu Bamalli shi ne jakadan Nijeriya a Ƙasar Moroko.

Haka nan, shi ne Magajin Garin Zazzau kuma ɗan uwa gs Mai Martaba Sarkin Zazzau.

By Editor