Shafi-mu-lera: Ya abin yake a kimiyyance?

Spread the love

Daga ABDULAZIZ TIJJANI BAƘO (MBBS, MPH, PhD)

An shafe shekaru ana azabtar da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba bisa zargin cewa sun sace wa wani ‘ya’yan maraina ko al’aurar wani namiji ta hanyar siddabaru ko tsafi.

A kan irin wannan zargi maras tushe an kashe mutane masu yawa, an kuma jikkata mutane da dama. Tarihi ya nuna cewa, wannan dabi’ar an fara ta ne a Nijeriya a shekarun 1970s sannan ta yaɗu a kusan dukkanin sassan ƙasashen Afirka.

A garuruwan Asiya akwai kwatankwacin irin wannan ɗabi’ar wacce su ke kira ‘Koro,’ duk da cewa lokaci zuwa lokaci akan ɗan samu varkewar cutar ƙasashen yamma jefi-jefi. Cutar Koro kamar annoba ce da ta ke sanya wasu sassa na mutane su haƙiƙance cewa tabbas al’aurarsu tana motsewa tana komawa cikin jikinsu, kuma su riƙa ji cewa idan ba a yi komai ba, al’aurar za ta ɓace ɓat ta shige cikin jikinsu. 

A lokuta da dama mutum ɗaya ne yake fara cewa ya ga al’aurarsa tana motsewa, kwatsam kawai, sai sauran mutane su ma su ga cewa su ma fa al’aurarsu ta fara motsewa. Irin wannan abu galibi matsala ce ta ƙwaƙwalwa (psychological problem) da kan addabi al’umma a lokaci guda wacce a je kira da  “mass hysteria.”

Sai dai bambancin “Koro” da shafi mu lera shi ne cewa, su masu Koro galibi ba wani suke zargin cewa ya yi musu asiri ba ballantana su kama wani wanda bai ji ba bai gani ba da duka.

Sannan kuma cutar Koro ba ta ta’allaƙa da maza zalla ba. Mata ma suna yi. Sai dai da ya ke maganar shafi-mu-lera muke yi, ba zan tsawaita jawabi a kan cutar Koro ba.

Da yawa daga cikin masu zargin cewa an yi musu shafi-mu-lera, sukan ce sun haɗu da wani mutum sun gaisa da shi. Sai kuma daga gaisawar suka ji wani abu ya yi musu yar a jikinsu kamar ‘shocking’. Daga nan kuma sai suka duba ‘ya’yan marainansu sai suka ji babu su. Daga nan kuma kawai sai su kwarma ihu.

Idan mutumin da suke zargi yana kusa su kama shi a yi ta duka. Idan azaba ta yi azaba sai wanda ake zargin ya yadda cewa ya aikata. Amma zai dawo wa mutum da abinsa bayan wani lokaci. Idan kuwa aka jirayi lokacin sai a ga ya dawo ɗin. Shikenan sai mutane su gaskata cewa tabbas satar ‘ya’yan marainan aka yi.

Kafin na yi bayani a kan yadda wannan abu ya ke faruwa a kimiyyance ya kamata na yi taƙaitaccen bayani a kan yadda ‘ya’yan marainan ɗan Adam suke samuwa tun yana ciki. Su dai  ‘ya’yan marainan ɗan Adam farko suna samuwa ne a can saman cikin ɗan Adam.

Daga baya suke sakkowa su yo ƙasa su zauna a cikin jakar yayan maraina (scrotum) kusa-kusa da lokacin da za a haifi mutum. Shi ya sa wasu yaran idan aka samu matsala a kan haife su da  ‘ya’yan  marainansu a ciki ba su sakko ƙasa ba (undescended testes).

A yayin da  ‘ya’yan maraina suke sakkowa daga ciki zuwa jakar yayan maraina, akwai abubuwa da yawa da suke biyo su ko don ba su kariya ko kuma don wasu dalilai. A cikin waɗannan abubuwa akawai wani nama da ake kira da suna ‘Cremaster Muscle’. 

Kafin mu faɗi aikinsa, wannan yaɗin nama na ‘Cremaster Muscle’ yana da kyau mu gane cewa su  ‘ya’yan  maraina ba sa son zafi ya yi yawa ko sanyi ya yi yawa, domin kuwa, aikin haɗa maniyyin dan Adam da a ke yi a cikin  ‘ya’yan  maraina (spermatogenesis) ba zai yiwu ba idan zafi ko sanyi ya yi yawa ba.

Saboda haka, sai Allah cikin ikonsa ya halicci shi wannan ‘cremaster muscle’ ɗin tare da sauran wasu abubuwa kamar Dartos muscle da suke tabbatar da cewa, zafi ko sanyi bai yi wa  ‘ya’yan  maraina yawa ba.

Idan zafi ya yi yawa, ‘cremaster muscle’ yakan saki jikinsa sai  ‘ya’yan maraina su sakko ƙasa su sha iska. Idan kuma sanyi ya yi yawa, sai ‘cremaster muscle’ ya motse ya ja  ‘ya’yan maraina sama kusa da cikin dan Adam wanda zai zame wa  ‘ya’yan  marainan kamar abin ɗumamawa. Wannan dalilin ne ma ya sa a ke bai wa maza shawarar su rage saka matsatstsun dan kamfe (panties) saboda kada zafi ya riƙa yi wa yayan marainansu yawa.

A halittar shi wannan cremaster muscle, akwai abinda a ke kira kuma ‘cremasteric reflex’, wanda ya ke janyo wa shi wannan ‘cremaster muscle’ ɗin ya motse ya ja  ‘ya’yan maraina sama-sama ba wai don saboda sanyi ya yi yawa ba. Abubuwan da suke jawo cremasteric reflex sun haɗa da, idan aka shafi wurin jijiyar da take bai wa shi ‘cremaster muscle’ saƙo, ko kuma abubuwa kamar matsanancin tsoro da sauransu.

A galibin lokuta shi wannan ‘cremaster reflex’ ba wani can sama yake jan  ‘ya’yan  maraina ba, amma akan samu a wasu tsirarun mutane cewa motsewar da ‘cremaster muscle’ ɗinsu ya yi yana da ƙarfi sosai (overactive cremaster muscle), wanda wannan ƙarfin motsewar zai iya sanyawa su ji kamar shocking a jikinsu, kuma ya ja  ‘ya’yan  marainan su koma can sama kusa da mafitsarsu (inguinal region) kamar za su koma can cikin ciki (ana kiran hakan retractile testes). 

Idan irin hakan ta faru za ta iya yiwuwa a nemi  ‘ya’yan  marainan a cikin jakarsu a rasa, amma ba wai sace su a ka yi ba. Suna nan a jikin mutum kawai dai sun yi can sama ne ta yadda ba za a iya jinsu a cikin jakar  ‘ya’yan  maraina ba. Kana zuwa wurin likita zai nuna maka inda  ‘ya’yan marainanka suka maƙale.

Idan an gane bayanin da na yi a sama, to sai mu ce abinda ya ke faruwa shi ne mutum ya gaisa da wani da bai sani ba. Kwatsam, kawai sai ya ji cewa fa ya yi kuskure don mutumin nan zai iya zama mai shafi-mu-lera. Kwatsam sai yanayin tsoro ya kama shi. 

Wannan ƙarfin tsoron da ya ji sai ya saka ya ji yar a jikinsa, shi ma cremaster muscle ya harba ya motse sai ya ji kamar an yi masa shocking a  ‘ya’yan marainansa sannan ya ja  ‘ya’yan marainansa sama. Daga nan kuma sai ya taba  ‘ya’yan maraina ya ji ko babu su ko kuma kamar sun motse daga yadda ya sansu da. Shikenan sai a kama wani da duka. Azaba ta sa ya yadda cewa ya saci  ‘ya’yan  marainan, sannan ya yi alƙawarin zai dawo da su.

Wannan abin zai kwantarwa da wanda ya ke zargin an sace masa kayan nasa. Shikenan bayan wani ɗan ƙanƙanin lokaci ya dawo hayyacinsa ya ji komai ya dawo normal (saboda hankalinsa ya kwanta, ba wai don wani ya sace masa wani abu ya dawo masa da shi ba).

Haka abin yake ga masu zargin an sace musu al’aura wai ta motse. Shi ma yanayin fargaba ne da tsoro ya ke sanyawa jikin dan Adam ya fara fitar da wasu sinadarai.

A gurguje, a jikin ɗan Adam akwai abinda a ke kira ‘sympathetic nervous system (SNS) da parasympathetic nervous system’ (PSN). Saboda sauƙaƙa wa mai karatu ya fahimta, shi SNS shi ke harbawa yayin da mutum ya ke cikin halin firgici da sauransu (fight and fright), shi kuma PNS shi ke harbawa a lokacin da mutum yake halin hutu da kwanciyar hankali. 

Don haka, a yayin da mutum ya ke cikin firgicin tsoron cewa an sace masa al’aura ko kuma al’aurarsa ta motse, wannan tsoron ba zai bari ya ji cewa al’aurar tana yadda take ba, saboda a lokacin ‘sympathetic nervous system’ ne ya ke aiki. Har sai ya samu nutsuwa hankalinsa ya dawo kansa sannan za a gane cewa babu abinda ya same shi.

A wannan rubutu na sauƙaƙe  abubuwa da yawa saboda na sauƙaƙa wa masu karatu yadda za su fahimta. Amma muhallush shahid shi ne cewa, babu wani abu wai shi shafi-mu-lera.

Mu guji azabtar da mutane babu gaira babu sabab saboda wai zargin an sace musu al’aura ko  ‘ya’yan  maraina. Duk inda mutum ya yi ihun an sace masa wani abu, a yi maza a garzaya da shi asibiti ya ga likita. Babu wanda ya sace masa komai. 

Abdulazeez Tijjani Bako, mai sharhi ne a kan al’amuran yau da kullum musamman na siyasa da zamantakewar al’umma. Ya rubuto daga ƙasar Amurka.

By Editor