Mun fita daga hannun ‘yan sari, mun faɗa hannun ‘yan sane

Daga BELLO MUHAMMAD SHARAƊA 

A kwanakin baya ne dai shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kaɗa ƙararrawa a cibiyar kasuwar NASDAQ, wato kasuwar zuba hannun jari “Stockbroking” ma fi girma a duniya. Bola Tinubu shi ne shugaban ƙasa na Afrika na biyu  da ya sake samun wannan dama da buga ƙararrawar NASDAQ. Ita wannan kasuwar tana birnin New York a ƙasar Amurka, masu hada-hadar kuɗi da cinikayya da kasuwanci suna dogaro da ita a kullum wajen lissafe-lissafe na tattalin arziki a faɗin ƙasashen duniya.

Na saurari jawaban Bola Tinubu a gurin buga ƙararrawar, sai na ji shi yana bayanin  an cire tallafin mai a qasarmu Nijeriya kuma an tsara yadda za a inganta darajar Naira da Dala, ya ce, duk  mai sha’awa zai iya kai kuɗinsa Nijeriya ya zuba jari, ranar da yake so ya kwashe kayansa zai iya ɗiba, babu wata fargaba. Sai kawai na kwashe da dariya. Na san zance kawai aka yi.

A can gefe guda kuma a zauren majalisar dinkin duniya, Bola Tinubu ya gaya wa Antonio Gutteres, shugaban majalisar cewa, yana aiki tukuru domin gyara Najeriya, ya gaya masa ko da a Nijeriya ana zaginsa, zai shanye duk wani tashin hankali da baƙin jini a kan abin da ya sa a gaba ba zai fasa ba. Nan ma sai na bushe da dariya. 

A ranar da Tinubu yake wannan zaurance, an sayar da Dala ɗaya a kan naira 995, a yau kuma ta haura haka. Za ka lalo Naira dubu, a ba ka Dala ɗaya kacal. Farashin man fetur ɗan Najeriya, wato ‘brent’ a kasuwar duniya ya kai Dala 95. Farashinsa na tashi a NASDAQ, mu ma a nan Nijeriya yana dada tashi. Su su ci riba, mu mu sha wahala.

A sabon lissafin da aka yi, ta bayan gida an dawo da Subsidy kuma daga watan Satumba zuwa Disamba, za a kashe naira tiriliyon daya da biliyan 600 domin tallafin man fetur a kan kuɗinsa na kasuwa naira 617 a Arewa KO 583 a kudu. Idan kuma aka bar fetur a kan kuɗinsa na kasuwa babu tallafi sai ya kai Naira 900 kowacce lita ɗaya. Nan ma na yi dariya, ‘yan sari, sun tafi, ‘yan sane sun kama.

Mulkin APC ƙarya da yaudara. A yi wa Turawa ƙarya da daɗin baki, a zo gida Nijeriya a gallaza wa jama’a, kuma a cika su da FARFAGANDA.

Bello sharaɗa, ɗan siyasa ne mai sharhi a kan al’amurran gwamnati da siyasa. Ya rubuto daga jihar Kano.