Tinubu ya naɗa sabbin kwamishinonin INEC na jihohi guda tara

Daga BASHIR ISAH

Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin kwashinonin zaɓe na jihohi (RECs) guda tara ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) na wa’adin shekara biyar.

Tinubu ya naɗa kwamishinonin zaɓen ne kafin daga bisani Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin nasu.

Bayanin naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce Tinubu ya yi naɗin ne bisa damar da Sashe na 154 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima, da Sashe na 6 na Dokar Zaɓe ta 2022 suka ba shi.

MANHAJA ta kalato cewar waɗanda naɗin ya shafa sun haɗa da:

Mr. Isah Shaka Ehimeakne — Kwamishinan Zsɓen Jihar Edo

Mr. Bamidele Agbede — Kwamishinan Zaɓen Jihar Ekiti

Mr. Jani Adamu Bello — Kwamishinan Zaɓen Jihar Gombe

Dr. Taiye Ilayasu — Kwsmishinan Zaɓen Jihar Kwara

Dr. Bunmi Omoseyindemi — Kwamishinan Zaɓen Jihar Legas

Alhaji Yahaya Bello — Kwamishinan Jihar Nasarawa

Farfesa Mohammed Yalwa — Kwsmishinan Zaɓen Jihar Neja

Dr. Anugbum Onuoha — Kwamishinan Zaɓen Jihar Ribas

Mr. Abubakar Fawa Dambo — Kwamishinan Zaɓen Jihar Zamfara

Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Tinubu na sa ran sabbin kwamishinonin su yi aiki da ƙwarewa tare da bin doka wajen aiwatar da ayyukansu.