Kotun Ƙoli: Gobe su Atiku za su san matsayinsu

Daga BASHIR ISAH

A ranar Alhamis ta wannan makon Kotun Ƙoli za ta yanke hukunci kan ƙarar da ‘yan takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam’iyyun PDP da LP, Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar inda suke ƙalubalantar nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu wadda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar masa da ita.

Daraktan Yaɗa Labarai na Kotun Ƙoli, Dr Awemeri Festus Akande, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Ya ce an ɗauki matakan tsaron da suka kamata domin tabbatar da lumana a ciki da wajen kotun.

Baya ga rashin gamsuwa da nasarar Tinubu, Atiku yana kuma neman kotu ta ba shi damar gabatar da kwafin takardun bayanan karatun da Tinubu ya yi a Jami’ar Jihar Chicago University (CSU), USA, wanda ya yi zargin takardun bogi Tinubu ya miƙa wa hukumar zaɓe ta INEC.