Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Babban Darakta na Cibiyar Bayar da Shawara ta ‘Civil Society Legislative Advocacy Centre’ (CISLAC) Auwal Rafsanjani, ya ce galibin malaman addini da ke zuwa bara wajen shugabannin siyasa su na zubar da mutuncin su.
Da yake magana yayin wata hira da aka yi da shi a wani shirin karin kumallo na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, Rafsanjani ya ce, al’ummomi da shugabannin addinai da ya kamata su tabbatar da adalci da zama ginshiƙin gaskiya a cikin al’umma sun zama ‘mabarata’ ga ’yan siyasa.
Ya ce, “A da, mun san yadda kakanninmu suka tsaya ga gaskiya. Za su fuskanci gwamna, ko minista, ko shugaban ƙaramar hukuma, ko darakta, ko shugaban ƙasa, su gaya masa gaskiya, ba ta hanyar cin zarafi ba amma ta hanyar lumana domin ya gaywa wasu kura-kuransa, amma a yanzu ba haka abin yake ba.
“Yanzu ku gaya mani, wa ku ke gani yana gaya wa shugabanninmu gaskiya, a boye ko a bayyane? Da wuya mu ga waɗannan abubuwan suna faruwa, kuma shi ya sa yanzu za ku ga cewa shugabannin addini sun zama mabarata a zahiri.
“Wani gwamna ne zai kira su, za su yi gaggawar zuwa wurinsa. A da, dole ne gwamna ya zo wurin shugabannin al’umma ko shugabannin addini a kowane irin matsayi da ya samu kansa. Amma a yanzu malamai sai dai su riqa rige-rigen zuwa gidan gwamnati.
“Ina tsammanin hakan ya lalata mutunci da iyawar da ya kamata su samu tare da yin taka tsantsan yayin da suke yin abubuwan da ba daidai ba.”
Rafsanjani ya kuma soki jiga-jigan Nijeriya da ake ganin sun rasa damarsu wajen fafutukar tabbatar da adalci, inda ya ƙara da cewa son abin duniya ya mamaye tunanin mutane da dama tare da raunana mutuncin tsarin gabaɗaya.
A cewarsa, maimakon yin Allah wadai da abin da jiga-jigan siyasa ke yi, malaman addini sun yi shiru suna rokon al’ummarsu da su yi wa waɗanda ke zaluntar su addu’a.
Ya ce, “Yawancin mutanen da suke da ikon faɗin gaskiya, kuna gaya musu ba gaskiya suke faɗi ba ko kuma kawai su yi shiru.
“Wannan babban ƙalubale ne, kuma za ku iya kallonsa daga masu ruwa da tsaki a Nijeriya. Malaman addini da ya kamata su faɗi gaskiya wani lokaci sai su yanke shawara su yi shiru su nemi mabiyansu su yi wa azzalumai addu’a. Su ma shugabannin al’umma su na cikin takalmi ’yan siyasa”.
