A daina yi wa ‘yan Arewa barazana ko mu hana ci gaba da jigilar kayan abinci zuwa Kudancin Nijeriya – Ƙungiya

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Wata ƙungiyar Arewa mai suna Northern Consensus Movement of Nigeria, ta yi barazanar dakatar da ci gaba da jigilar kayan abincin zuwa Kudancin Nijeriya.

Wannan gargaɗi na mazaunin martani ne ga wa’adin kwana 10 da mai rajin kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bai wa al’ummar Fulani makiyaya a baya-bayan kan su fice daga ƙasar Yarabawa.

Da wannan, ƙungiyar Arewar ta ce ta sha alwashin ɗaukar dukkanin matakan da suka dace domin hana ci gaba da kwashe kayan abinci daga Arewa zuwa Kudu.

Ta ƙara da cewa, dole Yarabawa mazauna Arewa su bar yankin muddin aka ci gaba da yi wa Fulanin wannan barazana.

Da yake jawabi kan batun a wajen taron manema labarai da suka shirya, Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Awwal Aliyu, ya ce, “Kwanan nan aka sako Sunday Igboho daga kurkuku amma har ya bai wa al’ummar Fulani mazauna ƙasar Yarabawa wa’adin su fita su bar musu ƙasa.

“Wannan karon, ƙungiyar Northern Consensus Movement of Nigeria za ta yi duk abin ya dace don hana haka, kuma idan ya ci gaba da wannan barazanar, zai zamana ba mu da sauran zaɓi da ya wuci bai wa Yarabawa mazauna Arewa su fita su koma yankinsu.

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta nemi a biya diyyar ‘yan Arewa da suka rasa rayukansu yayin zanga-zangar ENDSARs da rikicin kasuwar Shasha-Akinyele da kuma abin da ya shafi IPOB/ESN.

Ta bada wa’adi a kan a cimma buƙatunta ko kuma ta shirya zanga-zanga na ƙasa baki ɗaya, sanna ta hana ci gaba da kai abinci ya zuwa Kudancin ƙasa.

Haka nan, ta yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da sauran hukumomin da lamarin ya shafa, hukumomin tsaro har ma da tsoffin shugabannin ƙasa haɗi da majalisun dokoki na jihohin Arewa, da su sa baki don cimma buƙatun da ta daɗe tana nema daga gwamnati.

#

Za mu soke lasisin kamfanonin lantarkin da suka kasa tavuka qwazo a Nijeriya – Gwamnati
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta sabunta yarjejeniyar bayar da lasisin rarraba wutar lantarki da kamfanonin samar da wutar lantarki ba a Nijeriya.
Adelabu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wajen bikin buxe masana’antar samar da wutar lantarki ta Nijeriya, NESI, da ya samu halartar ‘yan kasuwar da masu ruwa da tsaki, NMPSR, na kwanaki uku a Abuja.
Ya koka da cewa shekaru 10 bayan mayar da vangaren wutar lantarki zuwa kamfanoni a watan Nuwamban 2013, masu gudanar da aikin sun kasa cimma burin da aka sanya a gaba.
Ya dage cewa ga ma’aikatan da ba su cika tsammaninsu ba, za a soke lasisin su.
Ya ce, “Na ambata cewa bayan shekaru goma, lasisin ya qare, kuma lokacin sabuntawa ya yi. Sabuntawa ba ta kaitsaye ba ne. Duk kamfanoni masu zaman kansu waxanda ba su cika abin da ake tsammani ba ba za su samu sabunta lasisin su ba. Dole ne mu san ko kun bi sharuxxan lasisin da aka ba ku.
“Na ambata a cikin jawabina cewa galibin qasashe ba sa mayar da tsarin samar da wutar lantarkin su zuwa wani kamfani daga tsara zuwa watsawa zuwa rarrabawa. Amma mummuna, mun yi wannan; ta yaya za mu yi aiki a kusa da halin da ake ciki don cimma manyan abubuwan da muka sa gaba da manufofinmu?
“Kuma na ce ba aikin mutum xaya ba ne ko kuma na masu ruwa da tsaki. Aiki ne ga kowa da kowa. Dukkanmu muna da rawar da za mu taka.
“Dole ne mu haxa kai mu taka rawar da za mu taka domin mu fito da qarfi da kuma samun nasara a masana’antar.
“Za mu duba qarfin fasaha na GenCos da DisCos. Za mu duba iya qarfin kuxi na DisCos. Nawa ka kashe tun lokacin da ka samu wannan lasisi? Nawa kuka yi ga abubuwan more rayuwa? Wace asarar AT&C kuka rage dangane da yarjejeniyar lokacin da aka ba ku lasisi? Wannan ita ce tattaunawa mai tsanani da ya kamata mu yi da masu gudanar da kamfanoni masu zaman kansu a rarraba da kuma matakin kamfanoni masu tasowa.”
Manhaja ta tuna cewa a watan Nuwambar shekarar 2013, an mayar da vangaren wutar lantarki zuwa wani kamfani, tare da kamfanonin samar da wutar lantarki guda shida da kuma kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11.

#

#

An rantsar da Natasha Akpoti a matsayin Sanatar Kogi ta Tsakiya
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dattawa ta rantsar da Zavavviyar sanata mai wakiltar mazavar Kogi ta Tsakiya, Barista Natasha Akpoti-Uduaghan, a matsayin ‘yar majalisar dattawa ta 10.
Natasha ta yi rantsuwar kama aiki ne jiya Alhamis, 2 ga Nuwamba, 2023, bayan ta karvi takardar shaidar cin zave daga Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Qasa (INEC) a matsayin zavavviyar Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya.
Akpoti-Uduaghan, wadda aka zava a Jam’iyyar PDP, ta zama Sanata ta farko daga jihar Kogi.
A ranar Talata ne Kotun Xaukaka Qara da ke Abuja ta tabbatar da Akpoti-Uduaghan a matsayin wadda ta cancanta a zaven Sanatan Kogi ta Tsakiya da aka gudanar a farkon watan Fabrairu.
Kotun ta yi watsi da qarar da Abubakar Ohere na Jam’iyyar APC ya shigar saboda rashin cancanta.
A watan Satumba ne kotun sauraron qararrakin zave ta jihar Kogi da ke zamanta a Lokoja ta soke nasarar Ohere a matsayin wanda ya lashe zaven Sanatan Kogi ta Tsakiya.
Kotun ta kuma bayyana Akpoti-Uduaghan a matsayin wadda ta lashe zaven Majalisar Dattawa da aka yi a watan Fabrairun da ya gabata.
Ko da yake Ohere ya garzaya Kotun Xaukaka Qara domin neman haqqinsa amma kotun ta qara tabbatar da Akpoti-Uduaghan a matsayin wadda ta lashe zaven.

Mataimakin Gwamnan Kebbi ya yi kira a qara qaimin tsaro kan iyakoki
Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Mataimakin Gwaman jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi ya yi kira ga hukumar kula da kan iyakokin Nijeriya da su qara qaimi wajen samar da tsaro kan iyakokin.
Ya yi wannan kiran a garin Sakkwato ranar Talatar da ta gabata a wajen wani taron qara wa juna sani da aka shirya don daqile ayyukan ta’addanci a kan iyakokin qasashen da jihohin da ke maqotaka da Nijeriya.
Sanata Umar Tafida wanda shi ne ya jagoranaci shirin ya ce ba shakka qirqiro wannan kwamiti zai zaqulo hanyoyin samar da tsaro da  zai taimaka wajen magance rashin tsaro kuma zai wanzar da zaman lafiya tsakanin al’ummomin dake zaune kan iyakokin.
Ya bayyana cewa jihar Kebbi tana aiki tare hukumar kula da iyakokin Nijeriya da ke vangaren ta wajen wanzar da zaman lafiya da kuma hulxar cinikayya mai kyau da qasashen Jamhuriyar Nijar da Benin da ke makotaka da ita.
Daga qarshe an shirya wani qudurin haxa hannu tsakanin hukumar kula da iyakokin Nijeriya da gwamnaticin jihohin da ke maqotaka da waxansu qasashe da kuma jami’an tsaro da sarakunan gargajiya don aiki tare wanda zai samar da tsaro da kuma zaman lafiya mai xorewa  da yaqi da ta’addanci da ke faruwa kan iyakokin.
Taron ya samu halartar mataimakan gwamnonin jihohin Kebbi, Alhaji Idris Muhammadu Gobir na Sakkwato, Alhaji Faruku Lawal na  Katsina da Injiniya Aminu Usman daga Jigawasai wakilai daga jihohin Zamfara da Borno da kuma Yobe da jami’ai daga hukuma Mai kulawa da iyakokin Nijeriya da kuma shugabannin qananan hukumomin Arewa, Augie, Dandi,  da sarakunan gargajiya da ke kan iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.
     

Sakataren Ilmi a Qaramar Hukumar Augie ya ja kunnen malamai
Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Sakataren Ilmi na Qaramar Hukumar Mulki ta Augie Malam Umar Umar Dankal ya ja kunnen malamai da mayar da hankali wajen aikinsu.
Ya yi wannan kiran ne ofishinsa da ke garin ranar Larabar da ta gabata sa’ilin da ya ke zantawa da wakilinmu.
Malam Umar ya ce malamai sun daxe suna kukan rashin samun waxansu haqqoqansu da kuma qarin albashi ko bayan samun cigaban matakin aiki daga gwamnatocin da suka gabata amma yanzu wannan sabuwar gwamnati qarkqashin jagoranacin Malam Nasiru Idris Kauran Gwandu ta xauki xamarar gyaran albashi tare da biyan haqqoqansu, saboda haka babu wani dalili da zai hana malami zuwa wajen aiki.
Ya qara da cewa a na su vangaren za su qara qaimi wajen ganin xaukar matakin da ya dace don ganin fannin ilmi ya farfaxo.
Malaman firamare su ne tubalin ilmi wanda kowa ta nan ne ya kan soma wannan shi ne ya bai wa Gwama Malam Nasir Idris kuzarin ganin ya kamata a gyara makarantu da kuma albashin malamai da sauran haqqoqansu a matsayinsa na malami.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su bai wa malamai haxin kai wajen kai yaransu makaranta, su kuma sarakuna su saka ido tare bayar da shawara a duk lokacin da suka fa wani abu da ya kamata a yi gyara a kai.

Akwai buqatar Tiriliyan N18 don gyaran titunan Nijeriya – Ministan Ayyuka
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Ayyuka, Dave Umahi, ya ce ana buqatar Naira tiriliyan 18.6 domin magance matsalolin da suka shafi harkar tituna nan da shekaru huxu masu zuwa.
Umahi ya yi wannan iqirarin ne a ranar Larabar da ta gabata, a gaban kwamitin majalisar wakilai kan kasafin kuxi yayin da yake kare Naira biliyan 300 na ma’aikatar daga qarin Naira tiriliyan 2.17 da aka yi akan kasafin kuxin bana.
A yayin da yake kira da a samar da kuxaxen gaggawa domin tunkarar matsalar tavarvarewar hanyoyin Nijeriya, ya ce “domin magance matsalar hanyoyinmu na tsawon shekaru huxu masu zuwa, za mu buqaci Naira tiriliyan 18.6, don haka dole ne Majalisar Dokoki ta yi amfani da qarfin tunaninta kan yadda za mu iya da gaske wajen magance matsalolin vangaren hanyoyinmu.
“Ina kira ga Majalisar Dokoki ta Qasa cewa ya kamata Majalisar Zartarwa ta mutunta qudurori da ku ke yi kan wasu kutse. Dole ne mu samu asusun gaggawa. Lokacin da kuka ce in je in sa baki a kan wasu hanyoyin da suka lalace, dole ne in kwatanta lamarin da wani mai taimakon rayuwa domin hanyoyin Nijeriya na buqatar taimakon gaggawa.
“A inda aka samu xaukin gaggawa, an yanke hanyar kuma ‘yan qasar na shan wahala; an dakatar da duk wani motsi. Yana buqatar shiga tsakani na gaggawa. Don haka, muna roqon a kawo xauki don mutunta umarninku kan daidaita al’amuran gaggawa,” in ji Umahi.
Umahi ya qara da cewa, Nijeriya na amfani da tituna a kashi 70 na zirga-zirgarta, abinda ke nuna da cewar akwai buqatar gyara fannin titunan qasar don cigaba da zirga-zirga.

By Editor