Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ministan Ma’adanai na Nijeriya, Dele Alake, ya ce, yana da ƙwarin gwiwa akam qwarewar Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a Alhaji Mohammed Idris Malagi wajen gudanar da aikin ma’aikatarsa kamar yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba shi.
Alake ya bayyana haka ne a ranar Alhamis lokacin da Malagi ya kai masa ziyarar ban girma.
Ya ce, Malagi ya cancanci naɗin nasa ne saboda halayensa na jagoranci da kuma rawar da ya taka wajen fitowar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
“Ba za a tava sanin irin rawar da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ya taka wajen kawo wannan gwamnati karagar mulki ba.
“Mun yi tafiya mai nisa kuma na yi farin ciki da cewa shi ne ke tafiyar da na’urorin bayanai na wannan gwamnati.
“Ni da kaina ina da cikakken kwarin gwiwa game da iyawarsa na cimma manufofin wannan ma’aikatar da kuma aiwatar da aikin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba shi,” inji shi.
