Alƙali ya gargaɗi jama’a da su daina jibge masa layu da kayan tsubbace-tsubbace a kotu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai Shari’a Hakeem Oshodi na Babbar Kotun Ikeja, Legas ya gargaɗi jama’a cewa su daina lavavawa su na jibge masu layu, kambu, karhuna da gurayen tsibbace-tsibbace a cikin kotu.

Oshodi ya bada wannan gargaɗin a ranar Litinin, yayin shari’ar wasu mutum biyar da ake tuhuma da kisan wani mai suna Ifeanyi Etunmuse.

A ranar Litinin ɗin ce dai aka fara shari’ar, inda kuma a ranar ya yi wannan gargaɗin.

“Kada wanda ya ƙara jibge min layu da karhunan tsibbace-tsibbace a kotu. Kada a kuskura a ƙara yi min haka. Domin an samu layu a zaman kotun da ya gabata kan wannan shari’ar,” cewar sa.

Mai Shari’a ɗin ya ƙara da cewa “kada wanda ya ƙara bar min tarkacen shirgin tsatsube-tsatsuben sa a cikin kotun nan. Saboda ba za su yi tasiri ko kaɗan ba.”

An dai gabatar da tuhume-tuhumen zargin laifin kisa da ake wa mutum biyar, waɗanda suka haɗa da Atunsare Omolabi, Shittu Olawale, Olaide Opeifa, Olanrewaju Adebiyu da kuma Jamiu Omosanya.

An zarge su da yunƙurin kisa da kuma kisan Etunmuse a Ijede, Ikorodu, Legas.

Tun farkon shari’ar, lauyan da ke kare waɗanda ake tuhumar ya ci gaba da yi wa mai gabatar da ƙara tambayoyi, wato Babatunde Olayinka.

Jagoran lauyoyin waɗanda ake tuhuma, ya tambayi Olayinka mai gabatar da ƙara idan har zai iya tabbatar da hannun waɗanda ake tuhumar wajen kisan mamacin.

An kuma tambaye shi ko idan ya na da hoton harabar farfajiyar gidan ɗan siyasar wanda aka kashe, wanda kuma ɗan kasuwa ne, wato Oluwatosin Onamade, wato inda ya ɓoye kafin a kai masa farmaki.

An kuma tambaye shi ko ya na da hoton lokacin da ake bizne mamacin a maƙabarta?

Ya shaida wa kotu cewa shi ma ya na cikin maƙabartar, kuma tare da shi aka ɓoye, a lokacin da makasan su ka fito da adduna, a gidan sa, a ranar 16 Ga Afrilu, 2021.

Ya ce a lokacin da ya ke ɓoyen ne ya juya bayan sa ya ga gawar mutum.

Bayan dogon Turancin bayanai da tambayoyi, Mai Shari’a ya ɗage ci gaba da sauraren ƙarar har sai ranar 19 ga Fabrairu, 2024.

By Editor