Duk matar da ba za ta yi sana’a ba ba ta san kanta ba – Fa’iza Badawa

Spread the love

“Rashin amincewa mace ta yi sana’a da mijinta zai yi ne kawai matsalar ta a kasuwanci”

Daga MUKHTAR YAKUBU

A yanzu da yanayin rayuwa ya sauya, a kullum a na ta kiraye-kirayen mata da su kama sana’a ko wani kasuwanci wanda za su dogara da kansu, musamman ma dai a gidagen zaman aurensu, duba da cewa, a wannan zamani da muke ciki ko mazan na shan kashi a hannun taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasa, ta yadda matsin rayuwa sai ta’azzara yake yi.

Hakan na daga dalilan da ya sa maza da yawa samunsu ya ragu, don haka hidimtawa iyali sai ya zama ƙalubale ga kaso mai yawa daga cikinsu, yayin da masu ɗan sauƙi daga ciki suka ja baya, ta hanyar rage rayuwar jin daɗi da suke ba wa iyalansu don samun damar daidaituwa da yanayin da ake ciki.

Da yawa wannan matsala ta girgiza gidajen aurensu, wasu mazan na kallon nauyin ya yi masu yawa, don haka suke sauke haushin kan iyalan nasu, da zaran an buƙaci wani abu daga gare su. Wasu kuwa matan ne ke ta tayar masu da hankali kan cewa, ba su kawo abinda ya kamata su kawo ba na daga hidimar gida.

Da wannan an ta samun mata suna yin yaji su tafi gidan iyayensu, ko su mazan su tunkuɗa ƙeyarsu zuwa gidan don su ɗan sarara. A wani ɓangare kuwa hakan har sanadiyar mutuwar aure ya yi.

Da wannan bayanin zan iya cewa ba lokacin da sana’a ga ‘ya mace take da muhimmanci kamar irin wannan lokacin, domin mata da yawa da mazajensu ba su aminta da su nemi na kansu ba a baya, idan sun ga yadda wasu matan ke hidimtawa gidansu da ɗan abinda suke samu albarkacin sana’a sai su dinga cizon yatsa, wasu kuwa wannan yanayi ya sa sun canza ra’ayinsu game da barin mace ta nemi na kanta, wasu ma da kansu suke ba wa matan jari don su fara sana’a.

Ita kuwa macen da ta ƙi neman na kanta, a wannan lokacin ne ta fahimci shayi ruwa ne, madara ake sa masa ya yi kauri. Ta gane abinda aka jima a sanar da ita game da neman na kai. Domin tana ji tana gani wani abin zai fi ƙarfinta, shi kuwa mijin da ta dogara, ta ɗora duk ɗawainiyarta kansa, shi ma ta kansa yake, tsadar shinkafa da taliya kawai ta ishe shi, don haka tana ji, tana gani ɗan na sayen kayan ƙyalƙyali da na data zai gagare ta.

Kar na cika ku da surutu masu karatu, kamar kullum shafin Gimbiya na zuwa maku ne domin ilimintarwa ga mata, tare da sa musu karsashi na son neman na kansu, ta hanyar karanta bayanai ko hirarrakin da muka yi da wasu mata. Kuma ta irin wannan ne za su iya samun ilimi kan hanyoyin da wasu suka bi don farawa, ko hanyoyin da ya kamata su kauce wa sakamakon wasu sun bi sun haɗu da ƙalubale.

A wannan makon shafin ya tattauna da macen da za ta zama hujjar da mata za su amince cewa, mata za su iya fara sana’a a gidan aurensu, kuma su iya miƙewa, ba kamar yadda wasu ke cewa, dole duk macen da ke son ta za ma wata abu a sana’a dole sai ta fara sana’ar tun a gidan iyayenta, ta yadda ko da za ta shiga gidan miji sana’ar ta soma ƙarfi.

Fa’iza Muhammad Badawa na ɗaya daga cikin matan aure da su ke gudanar da harkar kasuwanci a gadan mazajensu wadda ta fara da ƙaramin jari har kuma kasuwancin ya bunƙasa.

Domin jin yadda ta fara kasuwancin da kuma nasarorin da ta samu, wakilin Blueprint Manhaja a Kano, ya tattauna da ita, inda ya ɗauko batutuwa da dama dangane da rayuwarta baya ga batun yadda ta fara sana’a da kuma matakan da ta bi har ta kai ga matakin da ta ke kai yanzu. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta mu ta kasance;

MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatunmu.

FA’IZA BADAWA: Assalamu alaikum wa rahmatulla. Da farko dai sunana Fa’iza Muhammad wadda aka fi sani da Fa’iza Badawa. Ni ‘yar Kano ce. Kuma na yi karatuna a Kano. Na yi aure na a Kano.

To ko ya aka yi ki ka fara harkar kasuwanci a matsayin ki ta matar aure?

To ni daman ma’abuciyar son kasuwanci ce sosai, sam ban son zama haka ba na sana’a.
Bayan na yi aure na fara sayar da kayan kwalliya da takalma. Daga baya kuma na fara sayar da dogayen riguna da Hijabai na yara da na manya kala-kala sai wanda mutum ya zaɓa.

Wannan kasuwancin da ki ke yi ki na fita wani waje ne ki kasa kayan naki kamar shago haka ko a cikin gida ki ke yi?

A cikin gida na ke da shagon da na ke saida kayana mijina ya bani gudunmawa kala-kala a kan harkar kasuwancina ba ni da matsala ta wannan ɓangaran ko kaɗan, don haka ba abinda zan ce face Alhamdulillah. Hakan kuwa ya haifar min da nasarori a rayuwata kala-kala.

To ko wacce irin matsala matar aure ta ke samu idan ta na sana’a ko kasuwanci?

Idan kaga matar aure ta na samun matsala a harkar kasuwanci to dama mijinta bai amince ba ta ke yi. Ni kuwa mijina babu abin da zan ce masa sai dai godiya domin ya zama uwata ya zama ubana.

Yanzu wacce shawara za ki bai wa matan aure a game da sana’a?

Ai duk matar da ba za ta yin sana’a ai ba ta san wacce ce ita ba. Don haka mata ku tashi daga bacci ku nemin abin yi duk da a yanzu dai da yawa mata sun farga da neman na kansu.

Za mu so ki sanar da masu karatunmu matakan da ya kamata macen aure ta bi kafin ta fara sana’a a matsayinta ta matar aure?

Na farko dai sai kin tambayi umarnin mijinki kafin ki fara sana’a. Sannan in ba ki da jari za ki iya tambayar sa ya ba ki jari in yana da shi. In kuma ba shi da shi sai ki tambayi iyayyanki ko ‘yan’uwanki su taimaka miki.

Gaga nan sai ki fara. Sannan kuma dole sai kin sa tsoran Allah tunda kina da aure, a matsayin ki ta matar aure, ki san yadda za ki yi mu’amala da mutane musamman maza, idan ki ka yi hakan, sai ki ga komai yana tafiya daidai.

To madalla mun gode.

Ni ma na gode.

By Editor