Daga IBRAHIM GARBA NAYAYA
Nguru gururun duniya! Wannan yana daga cikin kirarin da muka taso muka ji ana yi wa wannan gari namu ma’abocin ɗaukaka da daraja! Gari, wanda ya samar da manyan mutane, shin malamai ne ko ‘yan kasuwa ne, ko wasu manyan ma’aikatan gwamnati! Gari, wanda ya yi shuhura da zaman lafiya da son addini da son masu addini! Gari, wanda mazaunansa suka taso suke ganin kowa ɗan’uwan juna ne!
Gari, wanda a baya za ka iske mazaunansa na bibiyar matsalolin juna domin su magance musu ba don su yayata ba! Gari, wanda mutum guda zai ɗauki nauyin karatu ko shayi (kaciya) ko kayan sallar mutanen unguwa sama da hamsin! Gari, wanda mazaunansa ke da karamci da karɓar baƙo sama da ko’ina a Nijeriya! Gari, wanda mazauninsa zai je baƙunta, kuma ya riƙe waɗanda ya kai wa ziyarar! Gari, wanda kowace mace ke rububin a auro ta a kawo ta, domin ta ɗanɗani lagwada da karamci da jin daɗi! Gari, wanda baƙon da ya zo ba ya son tafiya, wanda aka baƙunta ma baya son baƙon ya tafi!
Hohoho, wani kaya sai amale! Ga wanda bai san wannan ba, to ya bibiyi tarihi ko kuma ya jira fitowar littafin da muka adana waɗannan gwala-gwalan bayanai masu sanya zub da hawaye domin farin ciki! Amma domin bayar da satar amsa, bari mu hasko wasu zaƙaƙuran da wannan gari ya tattara, kuma suka yi amfani da damar su wajen ciyar da shi gaba:
Marigayi Alhaji Galadima Mai Dunoma (Sarauta/Siyasa) da Marigayi Alhaji Audu Sarkin Hausawa (Mahaifin Alhaji Zannah Maidodo) (Sarauta/Siyasa) da Marigayi Malam Mella Mai Takalmi (Malanta/Baduku) da Marigayi Alhaji Ibrahim Tsoho (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Maidami (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Inusa Mai Haja (Kasuwanci) da Marigayi Malam Inuwa Mai Ruwa (Siyasa) da Marigayi Alhaji Muhammadu Ɗanjaji (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Albishir (Kasuwanci/Siyasa) da Marigayi Alhaji Hamza (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Mai Iyali (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Ibrahim Mai Yi Dan Gaba (Mahaifin Alhaji Labaran Jika) (Kasuwanci/Siyasa).
Da Marigayi Alhaji Rabi’u Na Maigari (Kasuwanci) da Marigayi Malam Bura Mai Takalmi (Baduku) (Mahaifin Alhaji Malah Kasko) da Marigayi Mai Anguwa Ɗan Ƙiringa da Marigayi Alhaji Modu Sulum (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Tsalha (Kasuwanci) da Marigayi Malam Salihu Jakada (Kasuwanci/Malanta) da Marigayi Alhaji Dindin (Siyasa) da Marigayi Alhaji Dugu Balanguwa da Marigayi Alhaji Yaro (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Bukar Gana (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Babagana (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Dagari (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Bakabe (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Yakubu Kogar (Kasuwanci).
Da Marigayi Alhaji Garba Nayaya (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Ɗanhausa (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Abba Gajiramma (Siyasa) da Marigayi Alhaji Bukar Kilo (Siyasa) da Marigayi Alhaji Garba Ɓala (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Lawan Ngoma da Marigayi Alhaji Baba Kucici (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Buraji (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Salisu Garba (Kasuwanci) da Marigayi Alhaji Abacha Ngala (Tela).
A harkar karantarwa ma fa, ba a bar mu a baya ba, domin a garin ne aka sami manyan malamai a ɓangarori daban-daban irin su: Marigayi Sheikh Muhammad Ngibrima da Marigayi Sheikh Usman Fullatiya da Marigayi Sheikh Shariff Tahir (Malam Sharu) da Marigayi Malam Goni Karamsami da Marigayi Malam Manzo da Marigayi Malam Muhammad Shettima da Marigayi Malam Nafi’u Gangaran da Marigayi Malam Goni Yusuf da Marigayi Malam Modu Hafizi da Marigayi Malam Hassan da Marigayi Malam Goni Kime da Marigayi Malam Goni Musa da Marigayi Malam Goni Abba da Marigayi Malam Muhammadu Limamin Ɓaɓura da Marigayi Malam Garba Ɗandibe da sauransu masu yawa, wanda a yanzu ana nan ana ƙyanƙyasar wasu masu da’awa da karantar da al’umma addininsu.
Amma sai dai kash! Al’amarin a yanzu ya sauya, domin a yanzu matsaloi sun dabaibaye mu, ta yadda za ka kasa gane daga inda matsalar take, daga manyan ne ko yaran? Anyway, kowa dai yana da matsala, kuma matsala + matsala ne ke haɗuwa su zama matsaloli. Sai dai wani abin takaici, har yanzu babu wanda yake da tunanin a lalubo bakin zaren domin a ɗinke!
Shin, ina zumuncin da waɗancan mutane suka bar mana gado? Ina karantarwa maluman can? Ina son junan da aka shaide mu da shi? Ina kusanci da addinin da aka mana shaida da su? Ina karatun da muke yi, musamman wanda waɗancan maluma suka gadar mana? Anya an sami makwafinsu kuwa? Anya da za a haska musu abin da muke gudanarwa a yanzu ba za su tsine mana ba? Anya ba za su yi Allah wadai da mu ba? Anya ba za su yi baƙin ciki da mummunan sauyin da muka sa kanmu ba? Anya ba za su tuhume mu da cin amanarsu ba?
Idan ka ɗauki alƙalami domin yin rubutu, sai ka rasa me ma za ka rubuta! Da wane lafazi za ka yi magana domin ta gamsar da jama’a cewa akwai fa matsalar, wadda babu mai inkarinta sai ma’abocin jidali? Wacce matsala ma za ka tattauna? Su wa za ka fuskanta da matsalar?
Daga cikin ɗabi’un da aka yi tarayya a kai babu babba babu yaro illa man asal Laah, akwai hassada, ƙyashi, mugunta, ƙeta, zagon ƙasa, munafurci da kuma cin mutunci!
Idan ka ga muna kumfar bakin ba a yi adalci ba, to fa ba a yi mana abin da muke so ba, domin wai abin da muke so shi ne adalci!
Sau tari akan yi tarayya ba don a ture ƙarya da zalunci ba kasancewar an yarda ƙarya ne da zaluncin ba, ana yi ne domin wani son zuciya!
Daga cikin abubuwan da nake tsinkaya a rayuwa, ka ji tsoron wanda a kullum zai maƙale maka da sunan yana tarayya da kai a cikin sha’aninka, domin idan ya sami dama, shi zai fara kafa tubalin yaƙar ka!
Ya kamata shugabanni da manyan gari su zauna domin nemo bakin zaren ɗinke matsalolin Nguru, amma wallahi idan suka yi biris, muna ji musu tsoron ranar da dariyar su za ta zame musu kukan jini!
Matasa babu tarbiyya, ta ya ya kake tsammanin yaran da ke tasowa a yanzu za su zama kammamu?
Me ake tsammanin yawaitar ‘yan ƙwarya zai haifar a cikin irin al’ummar da muna ji muna gani babu wanda ya fi qarfin a je har gidansa a ci zarafinsa? Kuma a bar ‘ya’yan iska da ‘yan ta’adda su tafi, bal har a rinƙa ba su kariya!
Matsalar makiyaya da manoma abar a kalle ta ne kallo na tsinaki, ba wai a zuba idanu ba, domin zuba idanu kurum, da yin biris da abin, kan haifar da xa maras ido nan gaba!
Cin kashin da ake yi a wannan tsarin karɓar kuɗin wuta, wallahi ba za a yi a wani gari cikin garuruwan wannan Jiha ba! Me ya kawo haka? Saboda an raina shugabanninmu, ko kuma saboda su sun koma gefe suna faɗan matsayi da rikicin neman mulki, sun bar haƙƙoƙin da suka rataya a wuyansu! Ba wai ina nufin Shugaban gari kaɗai ba, duk wanda ke ɗaukar ma’anar shugaba, zai shiga wannan tarkon.
Wani abin takaici, duk ƙimarka da mutuncinka, yaro ƙarami ko ɗalibin da ka koyar wa ‘ha’ zai iya keta maka, kawai a dalilin wasu ‘yan siyasa ko wani ra’ayi na son zuciya ko kuma wanda bai ma fahimta ba! Wannan batu, ba fa labarin ƙanzon kurege ba ne, gaskiya ne! Domin mun ga yadda aka keta mutuncin Farfesa a dalilin son zuciya, irin yadda aka ƙona motar Malamin addini, kawai saboda wata maganar da masu wannan ta’addanci ba su ma fahimce ta ba! Amma da yake garin babu shugabanci a yanzu, har kawo yanzu shiru kake ji, tamkar maye ya ci shirwa!
Idan ka dube mu da kyau, za ka iske lalaci ta kowace fuska! Lalaci da cin amana a mu’amala! Lalaci da cin amana a zamantakewa! Lalaci da cin amana a tarbiyya! Lalaci da cin amana a tsarin karatu da makarantunmu! Lalaci da cin amana da tauye haƙƙi tsakanin yaro da maigidansa! Lalaci da cin amana a tsakanin ma’aurata! Lalaci da cin amana da rashin tsari ta fuskar shugabaanci da jagoranci da wakilci, face kaɗan cikin masu wakilci ko shugabanci!
Wallahi idan da shugabanni da manyan gari suna hango irin mustaqbal ɗin da muke hangowa wannan al’umma, na tabbata ba za su iya barci ba.
Ta Malam dai, ba ta wuce amin, a yanzu kam, namu kallo ne! Idan an ji zafin waɗannan kalmomi namu, to a yayyafa wa zukata ruwan sanyi, amma fa ba a canja wa tuwo suna ko da kuwa ya kwana an ɗumama shi!
Ibrahim Baba Ibn Garba Nayaya (Ph.D in view), Malami ne a sashen koyar da fasahar harsuna a tsangayar ilimin koyarwa a kwalejin malamai ta ƙasa da ke jihar Kaduna. Masani ne kuma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum musamman na siyasa. Ya rubuto ne daga Nguru ta jihar Jigawa. Lambar waya: 07066366586.
